Isa Yusuf Haruna da Abbas Suleiman, matasa ne da suka shigo da wani sabon salo na wakokin begen Annabi Muhammadu (saw) ta hanyar da aka fi sani a zamanance da Hip-Hop. ’Yan asalin Jihar Adamawa da Binuwai ne su amma mazauna Kano. Matasan, wadanda suka fara tashe a wannan harka, sun fadi dalilin da ya sa suka shigo da wannan salon a ganawarsu da Aminiya a makon da ya gabata. Ga yadda ganawar ta kasance:
Mutane na mamakin cewa kuna yabon manzon Allah (SAW) ta hanyar Hip-Hop, ko me ya sa kukeyin hakan?
Dalilinmu na yin haka shi ne cewa mun ga yadda matasa suke sha’awar Hip-Hop a yanzu. Idan ka karbi wayar matashi a yau, za ka tarar da wakokin Hip-Hop masu yawa a ciki. Ganin iri yadda matasan suka raja’a ga wannan salon waka, shi ya sa muka ga ya dace mu isar musu da sakonnin manzon Allah (SAW) ta hanyar abin da suka fi so. Ga shi dai Hip-Hop ne amma kuma manzon Allah (SAW) ake gaya masu a ciki.
Kafin ku fara amfani da wannan sabon salon waka, shin kun tuntubi malamai don sanin ingancin yin hakan?
kwarai kuwa, mun tuntubi malamai kuma sun tabbatar mana hallacin yin haka. Daga bayanan da muka samu shi ne cewa, hikimar nan da Allah Yake fada a cikin Alkur’ani mai girma cewa a yi kira zuwa tafarkinSa da hikima da kyakkyawan wa’azi. Don haka ne muka dauki wannan salon, shi ne abin da zamani ke aiki da shi tare da matasa. Domin da a bar matasa suna samun nishadi da sauraron abin da ba shi da amfani ta hanyar Hip-Hop, gwanda a ba su damar da za su nishadantu amma ta sauraron masoyinsu, fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW).
Idan kuka rubuta kasidarku, shin kuna kai wa gun malamai su duba su ga ko abin da kuke fada yana bisa ka’ida?
Da dai ba mu yin haka amma yanzu mun dau aniyar yin haka. Duk abin da muka rubuta za mu kai wurin malamai su duba, sub a mu tabbacin ingancinta, kafin mu fito da ita.
Na ga kayan da kuke sa wa ma irin na mawakan Hip-Hop ne, shin siffantuwa da irin kayan da suke sa wa ya dace?
Ai shi Musulunci addini ne da ya wuce gaban riga da wando. Imanin da ke zuciya shi ne abin da Mahalicci ke dubawa. Dalilin da ya sa muke shiga irin tasu shi ne, saboda cewa idan muka sa misali doguwar riga da wando irin na Bahaushe, matasa ba za su zo inda muke majilisi ba, domin ba shi ne a gabansu ba. Amma idan suka ga mun sa kaya irin na ’yan Hip-Hop, da farko za su zaci ’yan Hip-Hop din ne; don haka za su zo don su saurare mu. Amma suna zuwa za su ji yabon manzon Allah (SAW) muke yi.
Ya kuka ga karbuwar abin da kuke yi a wurin ’yan uwa Musulmi?
An karbi abin da muke yi kwarai da gaske, domin a duk inda muka je muka yi majalisi, za ka ga yadda matasa kan shiga shauki suna yi mana addu’a ta fatan alheri. Sannan a wurin za a sake gayyatarmu zuwa wani majalisin. Abin mamakin ma shi ne, har dattijai suna jin dadin abin da muke yi suna kuma sa mana albarka. Kuma dadin dadawa shi ne, matasan da ke sauraronmu sun hada da na kowace kungiyar addinin Musulunci.
Akwai wata riba ce ta abin duniya da kuke samu a sakamakon wadannan wakoki da kuke yi?
Mu manufarmu ita ce mu fadi waye manzon Allah (SAW) don Musulmi ya ji dadi, ya ji nishadi. Ba mu da wata manufa in ban da wannan. Don haka ne muke amfani da kudinmu mu buga waka kuma mu zo mu rera ta ga masu sauraro ba tare da mun sa wata ka’ida ta ijara ba.
Wane kalubale kuke fama da shi a wurin wannan sana’a ta kida da waka?
Babban kalubale yana zuwa ne daga wadanda ba su fahimce mu ba. Wasu lokutan akan sami mutum ya tare mu yace mana bai hallata a yabi manzon Allah (SAW) ta hanyar kidan Hip-Hop ba. Ko kuma idan aka ga mun sa kananan kaya sai a rika yi mana ganin mu wasu ’yan iska ne kuma abin mamakin shi ne cewa, masu kushe abin da muke yi, su ne masu sauraron wasu wakokin wadanda a wasu lokutan ma sabo ake yi a ciki. Sai dai duk wannan muna daukarsa a matsayin abin da duk aikin alheri ya gada ke nan. Shi ya sa muke yin hakuri a kai.
Wace shawara ko kira kuke da shi ga masu sauraronku?
Mu yardar mahaliccinmu muke nema ba yabon mutane ba. Don haka zargi ba zai yi mana wani tasiri ba. Fatarmu ita ce Allah Ya karbi abin da muke yi a matsayin aikin alheri ko kuma wata hanya ta isar da sakon Musulunci.