Asibitin Sultan da ke Titin Makarfi, a Unguwar Rigasa, Kaduna ya shirya gudanar da tiyata ga majinyata marasa galihu kyauta na tsawon mako guda daga ranar Lahadi 20 zuwa gobe Asabar 26 ga Agusta domin murnar dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari gida daga jinyar da ya tafi a Ingila.
daya daga cikin shugabannin asibitin, Dokta Tasi’u Ibrahim ne ya shaida wa Aminiya haka, inda ya ce za su yi tiyata ga masu fama da nau’o’in cututtuka biyar da suka hada da ciwon kaba na manya da ciwon kaba na yara da ciwon gwiwa da cire kitse daga masu ciwon teba da tiyata ga mata masu sankarar nono da cire kulu a hannun majinyata.
Dokta Tasi’u Ibrahim ya ce, “Za mu yi wannan aikin tiyata ne kyauta domin nuna godiya ga Allah Madaukaki da Ya dawo da Shugaba Muhammadu Buhari gida Najeriya lafiya domin ya ci gaba da aikin hidimar kasa. Wannan ya sa mu a Asibitin Sultan muka kudiri aniyar yin aikin tiyata kyauta ga marasa galihu na mako daya. Kuma muna rokon Allah Ya kara lafiya da basira ga Shugabanmu Buhari don ya yi wa kasa aiki.”
Dokta Tasi’u ya ce, tiyatar da za a yi kyauta ce, ba za a karbi ko kwabo ba, tun daga yankan kati da ganin likita da yin gwajin tabbatar da cutar da ke damun mutum da tiyatar da ba da magani da dawowa don ganin likita bayan aikin har zuwa warkewa. Ya ce, wadanda aka tantance ne kadai za a yi wa aiki ba wadanda suka zo lokaci ya kure ko wadanda cuta ta riga ta yi musu mummunar illa ba.
“Duk majinyata da aka tabbatar da abin da ke damunsu bayan an yi gwaje-gwaje da tantancewa ko suna da karfin jiki don jure wa tiyatar da majinyatar da aka dauki sunansu za a yi musu tiyatar ko da mako dayan da aka dauka ya wuce. Ma’aikatan da za su yi aikin sun hada da likitoci masu tiyata da masu yin allurar kashe zafin ciwo da masu tallafawa a dakin tiyata da masu gwaje-gwaje jini da nas-nas da kwararrun masu ba da magani da wadansu kwararru,” inji shi.
Ya ce ba wannan tiyata ce ta farko da asibiti ya yi magani ga majinyata kyauta ba. “Lokacin da Shugaba Buhari ya dawo daga jinyar farko, mun yi aikin tiyata kyauta ga masu fama da ciwon sukari da masu ciwon hawan jini, inda Shugaba Buhari ya samu wakilcin Ministan Harkokin Cikin Gida Janar Abdurrahman Dambazau, wajen kaddamar da aikin,” inji shi.
Dokta Tasi’u, ya ce suna yin wannan aiki ne don nuna kauna da soyayyarsu ga Shugaba Muhammadu Buhari tare da nuna godiya ga Allah kan dawo da shi gida lafiya. “Kuma muna yin haka ne don tallafa wa shirinsa na ’yan kasa su gina kasa mai taken” “Canji ya fara da ni,” inji shi.