Shugabar kungiyar Zawarawa da Marayu ta Jihar Bauchi Hajiya Rabi danladi ta ce abin da ya sa ta daukin nauyin wasu malaman addinin Musulunci domin karantar da alhazan Jihar Bauchi shi ne saboda yadda suke shan bakar wahala sakamakon rashin karantarwa a kan lokaci.
Ta ce “ana taron bitan ne daga karfe 4:00 na yamma ako wacce rana a makarantar Sa’idu Zungur da ke Bauchi kuma masu halarta za su sayi fom kan Naira 500 sannan kuma idan an kammala za mu raba musu satifiket,” inji ta.
“Na bude wannan makaranta ne domin yin bita ga alhazai na dauki nauyin biyan kudin alawus-alawus na malamai masu karantarwa.”
Daga nan ta ce mafi yawan wadanda suke amfana da taron mata ne wadanda suka fito daga yankin karamar hukumar Bauchi. Har ila yau, ta ce suna da burin fadada shirin zuwa wasu sassan kananan hukumomin jihar saboda “muna da kananan hukumomi 20 ne a Jihar Bauchi,” inji ta. Hajiya Rabi ta bayyana haka ne lokacin da take amsa tambayoyin wakilinmu a wajen taron wadda aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Shugabar ta ce suna gudanar da aikin tare da gudunmawar kungiyoyin addinin Musulunci kamar kungiyar Jama’atul Nasrul Islam da kuma hadin gwigwar kungiyar Izala ta jiha da makamantansu.
Ta ce: “Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Hadiza Abubakar tana daya daga cikin wadanda suka bani shawarwari domin ganin an shirya taron bitan kuma duk shekara za a rika karantar mata da maza domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba ba tare da ilimi ba.”
Abin da ya sa muka shirya wa alhazai taron bita – Shugabar Zawarawa
Shugabar kungiyar Zawarawa da Marayu ta Jihar Bauchi Hajiya Rabi danladi ta ce abin da ya sa ta daukin nauyin wasu malaman addinin Musulunci domin…