✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa muka ragargaza babura 482 – Gwamnatin Legas

Ya ce lalata baburan da suka yi na kan doron doka.

Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana na Muhalli a Jihar Legas, Shola Jejeloye, ya ce babura 482 din da suka kwace sannan suka ragargaza a Jihar sun yi ne a bisa kan ka’ida.

Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata cewa ba su lalata baburan don wata manufa ba, face sai don sun karya dokokin ababen hawa na Jihar Legas.

Idan za a iya tunawa, a cikin makon nan ne Gwamnatin Jihar ta lalata baburan guda 482 wadanda ta kwace a sassa daban-daban na Jihar saboda karya dokokin.

A cewar Shola, “Babu wani jin dadi da zan ji in na lalata dukiyar jama’a. Dokokin sufuri na Jihar Legas sun haramta wa ’yan acaba bin wasu tituna.

“Hakan ya hada da bin layin titunan da aka ware wa sauran ababen hawa da sauran motocin BRT, amma kullum wadannan ’yan acabar sai sun yi kunnen uwar shegu.

“Mu aikinmu shi ne mu tabbatar ana bin doka da oda, ba zai yiwu ka karya doka kuma ka ce doka ba za ta yi aiki a kanka ba,” inji shi.

Ya ce kwamitin na aiki ne a kan doron doka, bisa dokokin da gwamnati ta shimfida, inda ya ce Jihar ba kara zube take ba.

Ya kuma koka kan karuwar yawan matasa masu zaman kashe wando a Jihar, wadanda ya ce ba karamar barazana suke haifarwa ga harkar tsaro ba.