Hassan Yunus Abdulmalik shi ne babban Edita kuma babban jami’in gudanarwa na mujallar Al’ummata, a zantawarsa da Aminiya, Hassan ya bayyana tarihin mujallar da dalilin da ya sa suke buga mujallar da kuma kalubalen da suke fuskanta da kuma yadda yake ganin za a magance matsalolin, ga yadda zantawar ta kasance:
Aminiya: Ka gabatar mana da kanka a takaice?
Hassan Yunus: Sunana Hassan Yunus Abdulmalik. An haifeni a Kano, na tashi a Kano, na yi karatu a Kano, kuma na fara aikin koyarwa a Kano kafin daga bisani a shekarar 2013 na samu aiki da wani kamfanin samar da bayanai na wayoyin hannu a Jihar Legas a matsayin marubucin Hausa. Na rike wannan matsayi na tsawon shekara daya da rabi kafin a yi min karin girma zuwa babban edita na wannan sashe. Mukamin da har yanzu nake rike da shi ke nan a wannan kamfanin.
Aminiya: Ko za ka bayyana mana tarihin wannan mujalla ta Al’ummata?
Hassan Yunus: Tun bayan komawata Jihar Legas da aiki da kuma yanayin aikina da ya sanya kusan awa akalla 15 na kowace rana ina kan yanar gizo ne, shi ne sai na fahimce yadda al’amuran yada labarai da bayanai ke komawa kan yanar gizo. Na fahimci yadda kafafen yada labarai na yanar gizo ke kara karuwa a kullum, kuma kasancewar masu wadancan gidajen jaridu na yanar gizo ’yan Kudu ne, sai ya kasance labaran Kudu suka fi daukowa. In har ma sun dauko namu na Arewa, sai ya kasance babu wani wakilci na kirki da muke samu daga mujallun. Ina nufin mujallun sau da dama kan yada labaran kanzon kurege game da Arewacin Najeriya sakamokn ba su da wakilan da ke dauko musu rahotanni daga Arewa. Wannan ya sanya a shekarar 2016 na yi tunanin samar da mujallar yanar gizo ta Al’ummata (alummata.com) domin kishi da muka samar da labarai ingantattu da gyara tunani da fahimtar mutane da game da Arewacin Najeriya da ma kasa baki daya.
Aminiya: Kasancewa yanzu muna wani irin zamani da matasa sun fi son Turancin Ingilishi kuma kasancewa kana zaune ne a Kudu, me ya sa ka zabi ka bude mujallar ta harshen Hausa maimakon Ingilishi?
Hassan Yunus: Na zabi na wallafa al’ummata da harshen Hausa saboda abu na farko dai na fahimci akwai miliyoyin masu sha’awar karutu da son samun labarai da bayanai da harshen Hausa. Abu na biyu kuma shi ne, don in wakilci harshen Hausa ta hanyar samar da bayanai da daidai gwargwado za su fayyace hakikinin addini da al’adar Bahaushe.
Aminiya: Yaya kake yin kasuwancin mujallar kasancewa yawancin mutane ba su fiye son kasha kudi ba musamman a bangaren karance-karance?
Hassan Yunus: Kaso 70 cikin 100 na kasuwancin mujallar Al’ummata muna yinsa ne a kan shafin sada zumunta na zamani wato Facebook, domin na fahimci cewa a nan mafi yawan Hausawa suke. Amma muna kan sauran shafukan sada zumunta kamarsu twitter da Instagram. Ta haka ne muke isa ga abokan huldarmu, banda wadanda suke tuntubarmu watakila ta hanyar wani wanda ya sanar da su game da mu. A yanzu haka muna kokarin shiga wani tsari wanda da zarar mun yi rijista da wani kamfani, shi kamfanin ne zai dauki gabarar tallatamu ga masu son yin hulda da mujallun Hausa na kan yanar gizo a ko’ina a fadin duniya. Muna nan kokarin yin hakan.
Aminiya: Masu wallafa takardu da mujallu suna fuskantar matsalolin daban daban, wane irin matsaloli kuke fuskanta a wajen wallafa mujallar Al’ummana?
Hassan Yunus: A gaskiya ba zai yiwu kai tsaye na ce maka ba ma fuskantar wasu matsaloli ba. Sai dai, dama a tsarinmu mun shiryawa zuwan matsalolin ta yadda da zarar matsala ta zo, za mu tunkareta da niyyar warwareta cikin gaggawa. Wani lokaci za ka samu shafin ya ki budewa gaba daya na tsawon lokaci. A irin wannan lokaci, sai injiniyoyinmu su shiga aiki ka’in da na’in har sai sun shawo kan matsalar. Haka muke kokarin tunkara tare da magance duk wata matsala da ta taso.
Aminiya: Yaya kake ganin za a magance matsalolin da masu wallafa mujallu baki daya suke fuskanta kasancewar duk kanwar ja ce?
Hassan Yunus: Matsala ba abu ba ce da za ka iya kauce mata 100 bisa 100. Saboda haka, hanyar magance matsala daya tilo ita ce, shirya tunkararta da zarar ta faru da kuma tsara yadda za a a magance duk wata matsala kafin ta taso.
Aminiya: kasancewa mutane yanzu bas a son karance-karance duk kuwa da cewa akwai marubuta, meye kiranka ga al’umma a kan muhimmancin yawaita karance-karance?
Hassan Yunus: Akwai wani batu da a ke cewa idan har kana so ka boye ilimi ko wani bayani ga dan Najeriya ko dan Afirka, to, ka sanya bayanin a cikin rubutu. Wannan batu na nuna yadda dan Afirka ke da lalaci a wajen karatu. A gaskiya ya kamata a ce mu tashi tsaye mu dage wajen karance-karance domin dai ilimi da muhimman bayanai na cikin littattafai da rubutu ne. Da karatu ne za mu san abubuwan da duniya ke ciki kuma hakan ne zai ba mu ilimi da wayewa daidai gwargwado. Idan kuma ba haka ba, za a bar mu baya.
Aminiya: Ko kana da kira zuwa ga hukuma a kan yadda za a taimakawa marubuta da harkar rubuce-rubuce?
Hassan Yunus: Ya kamata hukumomi su shigo cikin harkar gina shafuffuka ko dai na yada labarai ko ma na wasu nau’ikan sana’o’in na daban domin dai yanzu duniyar ta koma harkar yanar gizo. Da taimakon gwamnati ne za a samu damar inganta tsarin ta yadda harkar yada labarai da bayanai cikin sauki zai yiwu kuma bisa tsari. A yanzu haka harka na neman zama ta ci barkatai saboda babu doka da oda, kuma an rasa doka da oda a tsarin ne saboda halin ko in kula da hukumomi suka yi wa harkar. Gwamnati za ta iya taimakawa masu wannan harka ta hanyar yin amfani da su a matsayin wasu hanyoyi na yada bayanan gwamnati zuwa ga jama’a a wani tsari na talla kamar dai yadda sukan yi ga jaridu ko mujallun da a ke bugawa a kan takarda.