Wasu matasa uku da ake zargi da ayyukan fashi a Jihar Osun sun shaida wa kotun Majistare da ke zamanta Osogbo cewa sun zabi shan tabar wiwi ne a kan sigari saboda kada su yi wa lafiyarsu illa.
’Yan sanda sun cafke wadanda ake zargin ne da safiyar ranar 3 ga watan Satumbar 2020 dauke da makamai suna zukar wani abu da aka yi ittifakin tabar wiwi ce.
Mazauna yankin sun tabbatar ce daya daga cikin wadanda ake zargin mai shekara 22 ya biye wa A ragowar mutum biyun masu shekaru 25 wajen tayar da zaune tsaye a garin.
An gurfanar da matasan ne a ranar Talata kan zargin yunkurin yin fashi da mallakar haramtattun makamai da kuma mallakar kulli-kulli na tabar wiwi.
Dan sanda mai gabar da kara Insifekta Elisha Olusegun ya shaida wa kotun cewa matasan sun yi kokarin aikata laifukan da suka sabawa sassan kundin penal code din jihar Osun na shekara ta 2002.
To sai dai wadanda ake zargin sun musanta zarge-zargen, inda a nan lauyan da ke kare su Tunbosun Oladipupo ya nemi kotun da ta bayar da belinsu.
Mai Shari’a Ishola Omisade ya bayar da belin kowannensu a kan N300,000 da kuma mutum daya da zai tsaya musu.
Ya kuma ya dage sauraron karar zuwa 8 ga wantan Oktoban 2020.