Daya daga cikin na gaba gaba a zanga-zangar da matasa suka shirya yi a ƙarshen wannan wata, wato Kwamred Murtala Gamji ya bayyana dalilin janyewarsa daga shirin yin boren.
Murtala Gamji wanda har ila yau jagora ne a Ƙungiyar Majalisar Matasa a Nijeriya ya bayyana hakan ne a yayin taron da jagorori daban-daban suka halarta don nisanta kansu da lamarin a ranar Laraba, a Abuja.
- Zanga-Zanga: An tsananta matakan tsaro a iyakokin Nijeriya
- Yadda Kirista ya taimaki mahaifiyar Rarara a hannun masu garkuwa
Ya ce, shirin zanga-zangar wanda ya biyo bayan ta’azzarar farashin kayayyakin masarufi da tsadar rayuwa sakamakon matakan da Gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ta ɗauka ya samu karɓuwa wajen wasu manya tare da ƙara faɗaɗa gabanin sauya aniyar tasu.
Sai dai a cewarsa ya zama dole su dawo daga rakiyar zanga-zangar bayan jagororin sun shaida masu cewa zanga-zangar za ta taƙaita ne kawai a birane uku da suka haɗa da Jos a Jihar Fulato da Abuja, sai kuma Kaduna, saɓanin jihohi 36 kamar yadda tun farko aka shirya.
“Wannan ne ya sa muke zargin cewa akwai lauje a cikin naɗi. Shin mai ya sa aka taƙaita shirya yin zanga-zangar a waɗannan yankuna uku na Arewa kaɗai.
“Babban burin al’ummar Arewa a yanzu shi ne a samar musu da tsaro da kuma yin wani abu a kan tallafin mai da a ka janye, don al’umma su samu zarafin komawa sana’ar noma da kiwo da aka san yankin da shi.
“Wannan shi ne kiranmu ga Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar da waɗannan buƙatu namu, idan hakan ya samu, harkokin kasuwanci za su bunƙasa a samu zaman lafiya a ko’ina’’, in ji shi.
A saƙon da ya aika wajen taron, Shugaban Majalisar Matasa na Jamiyyar APC shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham ya ce, amfani da hanyar tattaunawa tsakanin wakilan matasa da kuma gwamnati ita ce kaɗai za ta iya kawo mafita.
Alhaji Aburrahman Kwaccam ya ce, “Ya kamata matasa su kwana da sanin cewa, zanga-zangar da a ka shirya ba za ta haifar ɗa mai ido ga ƙasa da kuma al’ummarta ba, in ban da ma ta jefa al’umma a cikin ƙarin ƙunci da kassara tattalin arziki da kuma munana matsalar tsaro’’, in ji shi.
Ya buƙaci iyaye da jagororin al’umma da su ci gaba da faɗakar da matasa a kan illar zanga-zangar.