Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa sun daga maulibin bana da za a gudanar a Sakkwato da Abuja.
Shahararren malamin, wanda jagora ne a darikar Tijjaniyya ya ce, “abin da ya sa muka kira ku saboda abubuwan da suke faruwa a duniya, da mun sa rana za mu yi maulidin Shehu Ibrahim na duk duniya a wuri biyu a Nijeriya a Abuja da kuma Sakkwato, sai muka samu labari daga duniya cewa a wadansu kasashe an rufe masallatai, har kasar Morocco ma an rufe to makwabtanmu ma wadansu wurare an rufe filayen jiragen sama, kuma wannan taron namu ba mu ’yan Najeriya ne kawai ba, muna hadawa da mutane kasashen waje kuma ba su da ikon zuwa. To saboda haka muka dakatar da taron, har sai Allash Ya sa an samu lafiya, ko ina an warware an bude filayen jiragen sama, ko ina da koina ana tafiya sannan musa rana, yanzu kam ba mu san lokacin da za mu sa ranar ba. Amma dai mun dage taron ba za ayi shi ba saboda bala’in sabuwar cutar Kurona din nan.”
Ita dai wannan cuta ta kurona ta mamaye kusan duniya, inda a koina batunta kawai ake yi.