✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka ce kujerar hakimai ba ta gado ba ce – Gwamnatin Kaduna

Wane hali ake ciki bayan sanarwar da gwamnati ta bayar ta rusa hakimai da dagatai a Jihar Kaduna? Kamar yadda ka sani ne cewa wannan…

Wane hali ake ciki bayan sanarwar da gwamnati ta bayar ta rusa hakimai da dagatai a Jihar Kaduna?

Kamar yadda ka sani ne cewa wannan mataki da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka tuni ya fara aiki a masarautunmu 32 da gundumomin da abin ya shafa. Mun samu sakatarorin wadannn gundumomi suna lura da su kafin gwamnati ta tantance su wane ne za a nada. Kuma a kwanakin baya dama mun yi bayanin cewa wasu daga cikin masarautun sun sake kawo sunayen wadanda suke ganin sun cancanci a zabi wanda ya fi cancanta a cikinsu domin a nada shi hakimi. Yanzu abin da ake ciki ke nan. Kuma an fara tantancewar kusan mako biyu da suka wuce, a yanzu muna jiran rahoton abubuwan da aka samu a kan wadannan mutane da aka turo domin a zabe su. Da zarar an karbi rahotonsu gwamnatin jihar za ta kafa kwamiti domin tace wannan rahoto a zabi wanda Allah Ya bai wa wannan sarauta, sai a rantsar da su kamar yadda doka ta tanada. A nan akwai wadanda suka kai gwamnati kara a kotu, muna da kararraki kamar biyar, duk wani batu idan aka ce yana kotu ba a cika son yin magana a kansa ba, saboda kada alkali ya ga kamar ka yi masa shishigi.

Amma abin da ya sa muka kawo wannan magana shi ne domin mun samu uku daga cikin masu karar nan sun rubuta takardar janyewa, domin a cewarsu ba su san da wannan magana ba. Sun ga sunayensu ne kawai an ce wai suna karar gwamnati amma ba da hannunsu aka yi wannan batu ba. Sai ya zama idan mutum ya ce ba da hannunsa aka yi ba kuma an kaio kotu ka ga ya kamata mu samu hujja. Sai muka sa su rubuta sun kuma rubuta takardar wanda za mu yi amfanui da ita a kotu.

 Sannan ga shi wadansu suna kotu amma kuma sun rubuta takarda suna son a sake nada su, ka ga an yi ba a yi ba ke nan. Saboda haka lauyoyi sun tantance su za mu shiga kotu da shi. Abin da ke nan zan iya fadi a kan wannan batu da ke kotu. Sai dai karin bayani a nan shi ne matakin da gwamnati ta dauka mataki ne da ke bisa doka, domin dokar Jihar Kaduna ta bai wa Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna damar daukar wannan mataki da ya dauka.

Kuma abin da ake nema daga gare shi, shi ne ya sa hannu a kan dokar ta duba a wasu wurare suna cewa wai ai ba a kai majalisa ba saboda haka an taka doka domin kamata ya yi a ce Gwamna ya kai majalisa. Amma abin da suka kasa fahimta shi ne babu wata kujera ta hakimi ko dagaci da aka taba kai wa majalisa aka tantance shi. Doka ta bai wa Gwamna damar ya kirkiro wadannan masarautu sannan ya tabbatar da wanda Allah Ya ba shi, kuma wannan muka yi.

Ka ga wannan kwafin dokar ce ya zama daya daga cikin kundin dokokin Jihar Kaduna.

Duk magangnun da ake yi wai ba a kai majalisa ba jama’a ne kawai ke yi, amma abin da muka sani shi ne kamar yadda kotu ta umarta mun tura lauyoyi daga ma’aikatar shari’a domin kare gwamnati da jami’an gwamnati da aka kai kara.

Wani abu da ya ja hankalin jama’a a kan dokar shi ne batun cewa kujerar hakimi da dagaci ba ta gado ba ce. Me za ka ce a nan?

Wato ita sarauta da masarautu wurare ne da suka ginu bisa tarihi saboda haka daya daga cikin abubuwan da masarautunmu ke takama da shi, shi ne ka ga wani ya duba ya ce wai wannan kujera ta shekara dubu kuma za a iya fada maka daki-daki cewa wannan sarki ya bai wa wancan, wancan ya bai wa wannan. To, idan aka duba baya a tarihin masarautu wanda aka sani shi ne daga sarkin yanka sai dagaci da kuma mai unguwa.

Da tafiya ta yi nisa shi dagaci akwai wanda ake biya albashi da wanda ake kira gorori da ba a biya. Masu unguwanni dama tun farko ba su cikin masu albashi. Hakimai a lokacin da Turawa suka zo sai suka duba nasu da akan canja musu wurin aiki a matsayin ma’aikata. Da tafiya ta yi tafiya ne za ka ga hakimi ya zauna wuri daya har sai mutuwa ta zo ba a juya shi. Ba kuma wannan gwamnati ce ta fito da dokar nan ba, domin takarda muka tarar wadda Mai martaba Sarkin Zazzau ya rubuto wa Gwamna, wadda a shekarar 2001 Sakataren lokacin ya rubuta wa dukanin masarautun da muke da su cewa ana son ankarar da su cewa lallai mukamin hakimi ba na gado ba ne, saboda haka idan har aka samu wani yana yi ta yadda za a zabi wani hakimi duk wanda yake wannan gunduma da ya ga ya cancanta yana iya rubutawa ya nemi kujerar. Idan an tantance shi har aka ga ya dace za a nada shi a matsayin hakimin, ka ga ke nan tun a wancan lokaci ya nuna cewa mukamin hakimi ba mukami ne na gado ba. Kowa zai iya fitowa ya nema a ba shi. Shi ne kuma aka sake jaddadawa a nan, ke nan babu wata doka da aka taka. Illa ma an kara jaddada wani al’amari ne da ya jibanci sarauta ta gargajiya da ke neman ya bata aka sake farfado da shi.

An ce wanda aka sauke zai iya sake neman kujerar, sai wadansu ke ganin ina amfanin sake bai wa wanda aka kora damar neman kujerarsa. Ai da sai ku bar su kawai su ci gaba, me za ka ce?

Yauwa shi ma nan akwai hikimar da ta sa gwamnati ta ce haka, idan ka lura su gundumomin muna da 390 sai suka dawo 77. Misali su 77 din nan idan ka dauki Gundumar Kawo a yanzu ta fi Gundumar Kawo girma lokacin da muke da 390, to shi kuma Hakimin Kawo da aka tantance shi an tantance shi ne a wani dan takaitaccen wuri na kasarsa wanda yake a yanzu ya sake fadaduwa.

Saboda a ba da adalci ga wadannan wanda yake a da suna Gundumar Kawo a misali a ce tsohuwar Gundumar Kawo tana da gundumomi uku ka ga hakimai uku ke nan to, yanzu ta sake komawa matsayinta na tsohuwar Gundumar Kawo guda daya. Ka ga guda biyu sun rasa aiki, wadannan guda biyun ai ba laifi suka yi wa gwamnati ba, saboda a ba su damar su nemi wannan kujera sai aka ce bari a sauke su dukansu su uku watakila ma wanda gundumarsa aka rushe ba ya fi kwarewa ba ne a kan wanda ba a taba gundumarsa ba.

Idan aka ce wancan ba sai an tantance shi ba, sauran ba za su ga an yi musu adalci ba. Sannan jama’a kuma ba za su yi tunanin samun nagartaccen hakimi ba da zai shugabanci al’amuransu. Shi ya sa aka ce kowa ma ya sauka sannan a sake tantancewa. 

Har yanzu wadansu daga cikin hakiman da aka ce an sauke ana ganinsu suna halartar tarurruka kuma ana gabatar da su a matsayin hakimai. Ko kuna sane da haka?

Mun samu wannan bayani wanda hakan ya sa muka kira sakatarorin wadannan gundumomi muka kara nanata musu cewa dokar nan da gwamnati ta kafa tana nan, saboda haka wadannan sakatarorin gundumomi aka dora wa alhakin lura da ofishoshin hakiman kafin wadanda aka nada su zo. Abin da ya faru mun samu labarin cewa saboda wannan kara da wdanasu daga cikinsu suka shigar inda kotu ta ce kowa ya tsaya a inda yake. To, idan aka ce a tsaya inda kowa yake gwamnati ta riga ta sauke wadancan hakimai tun kusan mako biyu, kafin a ba da wancan umarni na kotu. Kada dai a yi zaben

Ne, amma dai su tsaya a nan. Don haka wadansunsu na ci gaba da zuwa amma dai suna zuwa ne kawai don kansu, domin hukuma ko a matakin kananan hukumomi sun san cewa an rigaya an sauke su kuma babu wata alaka da suke da ita a matsayinsu na hakimain wadannan wurare. 

Muna ta kokarin ankarar da jama’a su fahimci wannan tsari, in kuma akwai abin da suke neman gabatarwa a ofishin hakimi to, su samu sakatare wanda aka ba shi alhakin kula da wannan gunduma na wuncin-gadi shi ne zai saurare su. Idan har ta kama shi zai yi hulda da karamar hukuma sai ya shige gaba a je a yi da shi. Kuma a nan ma’aikatarmu sakatarori ke wakiltar wadancan gundumomi, ka ga ba mu san da wadansu na zuwa ba domin ba za ka hana mutane ganawa da jama’a ba, amma a gwamnatance ba mu da wata alaka da su.

Wadansu na ganin rushe su zai iya shafar harkar tsaro a wadancan gundumomi nasu idan aka yi la’akari da gudunmawar da suke bayarwa a cikin jama’a, me za ka ce?

Kaduna inda dama can babu zaman lafiyar bayan sauke mutanen nan sai aka sake samun ingantaccen zaman lafiya. Dalili shi ne a yau a Jihar Kaduna muna da masu unguwanni kusan dubu 22 suna nan suna aikinsu yadda ya kamata. Muna da shugabannin addini na Musulunci da na Kiristanci wadanda ba zan iya fada maka yawansu ba. Wadannan masu unguwanni da shugabannin al’umma suna da alaka dagatai su dagatan nan muna da 1,429 suna ofishoshinsu suna ayyukansu.

 Idan ka lura kamar yadda na fada maka mukamin hakimi, mukami ne na wanda ke lura da wadancan dagatai din, shi kawai nasa ya tsaya ne idan akwai wani abu da dagaci ya kasa warwarewa za a hadu a wurin Sarki shi zai zama kamar mai shiga tsakanin dagaci ne da Sarkin yanka. Sai muka ce ga shi yanzu babu hakimai amma akwai masu aikin da hakiman ke yi, ka ga babu wata barazana da rashin wadancan hakimai zai kawo shi nake son nanata maka. 

Kuma su aikin hakimai da dagatai aiki ne na kananan hukumomi sannan akwai jami’an da ke lura da wadannan kananan hukumomi 23, akwai jami’an da ke shugabantar rukuni-rukuni na karamar hukumar da suke zaune. Sannan a kowace gunduma akwai ofishin DPO na ’yan sanda akwai ’yan sintiri da yawa sannan a unguwanni, jama’a na shirya kansu domin samar da tsaro.  

A bisa rahoton da muka samu yanzu babu wani wuri da aka ce an samu matsala saboda rashin hakimi.

Wane kira kake da shi ga jama’ar Jihar Kaduna?

Kirana ga jama’ar Jihar Kaduna shi ne kamar yadda Gwamna Nasir El-Rufa’i ke ce musu kowane lokaci cewa wannan gwamnati tasu ce su suka zabe ta kuma tana aiki ne domin jama’a. Kuma a shekara biyu da aka yi jama’a sun tabbatar wannan gwamnati tasu ce, domin a cikin mazabu samad da 200 da muke da su, babu inda ba a aiki. A cikin mazabun ’yan majalisar jiha 34 babu inda wani dan majalisa zai ce babu wani gagarumin aiki da gwamnati ba ta yi a mazabarsa ba. La’lla yana jam’iyya mai mulki ce ko ta adawa. Wannan wani abu ne da al’ummar jihar suka dade ba su ga irinsa ba. Abin da ya rage shi ne a ci gaba da bai wa gwamnatin nan goyon baya a matakan jiha da kananan hukumomi ko ta tarayya. A kuma ci gaba da yi wa shugabanni addu’a saboda Allah Ya ci gaba da ba su kwarin gwiwa da basira domin gudanar da mulkin jama’a cikin adalci.