Tsohuwar shugabar mata ta rikao na kungiyar Kwankwasiyya Ideology, Hajiya Zainab Buba ta ce sun bude sabuwar kungiyarsu ta Kwankwasiya bolunteers ne domin fadada akidar Kwankwasiyya.
Hajiya Zainab ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da wakilin Aminiya a Kaduna, inda ta bayyana cewa ita akidar Kwankwasiyya ta wuce maganar siyasa kawai kamar yadda mutane suke tunani.
“Kwankwasiyya akida ce ta samar da cigaba ga al’umma da taimakon juna. Mutane suna tunanin cewa siyasa ce kawai. A’a, wannan wata kungiya ce kawai da ta hada mutane masu akidar samar da cigaban kasa da mutanen kasa,” inji Hajiya Zainab.
Da wakilin Aminiya ya tambayet a batun alakar kungiyar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sai ta ce “Maigida sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne jagoran wannan tafiya a duk fadin duniya, domin mu yanzu ba maganar Najeriya muke yi saboda shi kullum manufarsa ita ce gyara da taimakon al’umma.
“Yanzu duk inda ka zagaya a Najeriya sai ka ga mutane da jar hula, ko jan mayafi, wanda ke nuna alamar Kwankwasiya. Hakanan ma akwai wakilanmu a kasashen waje.
“Muna da kungiyoyi da yawa, amma duk manufar daya ce: Wato samar da cigaban kasa da taimakon al’umman. Babban burinmu shi ne kowa ya yi koyi da halaye da akidun Kwankwasiya, domin halaye ne masu kyau da suka hada da taimakon al’umma, samar da cigaban kasa, tallafawa marasa karfi, da dai sauransu”.
“Yawanci idan ka ga dan Kwankwasiyya, za ka ganshi yana son taimakon mutane, ashe ke nan, duk wani mutumin kirki zai so ya yi alaka da wannan kungiya ko akida.
Hajiya Zainab ta kara da cewa, shi Sanata Kwankwaso duk wanda ya sanshi ya san cewa mutum ne mai burin ganin mutane cikin walwala da jin dadi, musamman talakawa marasa karfi “Shi Sanata Kwankwaso dole a yaba masa bisa yadda yake aiki tukuru wajen ganin cewa kowane dan kasa ya ci moriyar arzikin kasar, ba wai sai ‘ya’yan manya ba. Shi ya sa a kullum yake fafutukar ganin cewa ya taimakawa ‘ya’yan marasa karfi, domin suma su yi karfi, su tallafawa iyayensu, ‘yan uwansu da ma kasa baki daya.
“Wanna ne ya sa muka bude wannan sabuwar kungiya domin mu fadada akidar, kuma mu kara samun mabiya a tafiyar Kwankwasiyya ta kasa baki daya,” inji Hajiya Zainab Buba.