Wata kungiyar matasan arewacin Najeriya ta ce kaunar da galibin mambobinta ke yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ce kadai ta sa ta lale kudi har N100,000 ta bai wa Dauda Kahutu Rarara don ya wake shugaban kasar.
Kungiyar mai suna Muryar Talaka ta bayyana haka ne ta bakin shugabanta, Alhaji Zaidu Bala Kofa Sabuwa, wanda ya tura kudin asusun ajiyar Rarara na banki.
- Yadda Rarara Ya Tayar Da Kura Kan Sabuwar Wakar Buhari
- Sai Masoya Buhari Sun Biya Zan Saki Sabuwar Waka —Rarara
“Ba dukkanin ’yan kungiyarmu ne masoya Shugaba Buhari ba, amma kashi 90 cikin 100 masoyansa ne”, inji Alhaji Zaidu.
A makon jiya ne dai Rarara ya ce zai shirya wa Shugaba Buhari sabuwar waka, amma ba zai yi bas ai masoya shugaban kasar sun ba shi N1,000, kuma kungiyar Muryar Talak ana cikin wadanda suka shelanta ba da kudin.
Kowa da kiwon da ya karbe shi
Wasu ’yan Najeriya dai na zargin cewa ta yiwu wani dan siyasa ne ya fake da wasu mutane ya ba da kudin don kada a ce masoyan Shugaba Buhari sun kare.
Sai dai a cewar Alhaji Zaidu, “ai da ma ba a iyankance wadanda za su iya bayar da gudunmuwar ba, an dai nemi dukkan masoya Buhari da su bayar da gudunmuwa walau babba ko karami”, inji shi.
Akwai ’yan Najeriya kuma da suka gwammace su kona kudin a kan su bai wa Rarara. Wadanda bidiyon su ya yi yaywo a kafofin sadarwa na zamani.
A ganin Alhaji Zaidu, “dama ai kowa da irin kiwon da ya karbe shi, kuma [’yan kungiyarmu] ba za su daina goyon bayan Shugaba Buhari ba saboda gwamnatinsa ta tallafa wa matasa a fannoni daban-daban.
“Sabanin gwamnatocin baya, gwamnatin Buhari ta kawo shirye-shiryen tallafi ga matasa ba tare da la’akari da akidar siyasa ta wadanda za su ci moriyarsu ba irin su N-Power, daukar ma’aikata 1,000 daga kowace karamar hukuma, tallafin noma da sauransu.
Kuncin rayuwa
“Idan kuka duba a lokacin baya, an kawo shirin Sure-P wanda kadai ya takaita ga wadanda ke goyon bayan gwamnati sabanin yadda ta kasance a gwamnatin Buhari da babu ruwanta da wadanda za su ci moriyar tallafin da kawo koda kuwa suna adawa da ita.”
Sai dai shi ma jagoran kungiyar ta Muryar Talaka ya amince talakwa na shan wahala. yana mai kira da gwamnatin Buhari ta yi la’akari da halin kuncin rayuwa da al’ummar kasa ke ciki musamman duba da irin mummunan tasirin da annobar coronavirus ta haifar.
Ya kuma nemi gwamnati ta bude iyakokin kasa saboda abinci ya yi karanci, yana cewa sai “ciki da ruwa ake iya janyo guga.
“Ya kamata gwamnati ta bude ‘bododi’ a shigo da abinci saboda abinci ya fara karanci ga kuma ambaliyar ruwa da muke fuskanta a kasar wadda ta ke lalata amfanin gona.”
Ana ta rade-radin cewa mawakin na siyasa ya tara kudi sama da Naira miliyan 7, amma a wata hira da ya yi da Aminiya ya ce kudin da aka samu ya wuce abin da ake hasashe nesa ba kusa ba.