✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Abin da ya sa mijina ya kashe kansa’

An taba kai shi neman magani a kokarin gyara masa hali.

Malama Hadiza Chedi, matar marigayi Lawal wanda aka fi sani da Kawu, wanda ya kashe kansa a Daura Jihar Katsina ta ce, mijinta ya yi fama da damuwa kafin ya aikata hakan.

Malama Hadiza ta bayyana wa Aminiya cewa, mijinta ya samu kansa a wani hali na shaye-shayen miyagun kwayoyi sama da shekara 15 da suka wuce.

“Mun yi aure shekara 20 da suka wuce, amma kimanin shekara 15 da suka wuce ya kamu da rashin lafiya amma ba mu da cikakkiyar masaniyar abin da ya same shi.

Mun zo Asibitin Kwararru na Tarayya da ke Katsina, bayan gwaje-gwajen da likita ya yi, ya shaida mana cewa yana fama da zazzabin cizon sauro wanda yake hana shi yin barci yadda ya kamata.

A lokacin mahaifiyarsa tana da rai, sai ta dauke shi zuwa Damagaram a Jamhuriyyar Nijar domin yi masa maganin gargajiya, amma babu wani sauki ko canjin da aka gani.

Har ila yau, an kai shi wajen Dokta Aliyu wanda shi ne mutum na farko da cutar Coronavirus ta kashe a Daura, bayan ya yi bincike ya ce, yana fama da matsala a cikin kwayoyin jininsa, nan ma aka kwantar da shi amma dai babu wani ci gaba,” inji ta.

Yadda kwayar Tramol ta zame masa jiki

Malama Hadiza ta ci gaba da cewa, “Wata rana na je bikin suna, muka yi zai je ya dauko ni amma har karfe 9:00 na dare bai zo ba.

Ganin haka ya sa na taho gida. Lokacin da zo na tarar da kofar gidan a rufe. Na buga har na gaji ba a bude ba har sai da na samu wani ya haura ta katanga ya shiga ya bude mini na shiga.

Bayan na shiga na tarar da shi yana barci, da na tayar da shi na tambaye shi ko lafiya, sai ya ce, mini babu komai.

Da na matsa da tambayar abin da yake faruwa ne ya ce mini wani mutum ne ya ba shi wani magani ya sha.

Farko ban damu da sanin irin maganin ba, amma daga baya sai muka gane cewar kwayar Taramol ce, wadda ita ce ta zame masa jiki.

Ta ce, “An taba kai shi Kofar Kaura a Katsina don yi masa magani tare da kokarin gyara masa hali.

Ya yi tsawon wata biyar, abin kamar an dace, amma daga baya sai abin ya sake dawowa, inda ya kai fagen ya shiga cikin shan manyan miyagun kwayoyin, halin da ya sanya shi shiga wancan yanayi na bakin ciki da damuwa.

Kuma tun daga wancan lokaci ya zamo ba ya son shiga ko zama a cikin mutane, kowane lokaci yana zaune shi kadai.

Har akwai wanda ya taba ba shi shawarar cewa ya je Kaduna domin neman magani.

Hakan ya faru ne saboda rashin shiga cikin mutanen a lokacin da ya fahimci bai iya rayuwa ba tare da ya sha kwaya ba.

Sannan yana da wuya mu yi zaman awa daya muna magana a tsakaninmu.”

‘Ba talauci ba ne dalili’

Dangane da zargin cewa, talauci ya sa mijinta ya kashe kansa, Hadiza ta ce, “Ma’aikaci ne a Karamar Hukumar Sandamu kuma yana rike da mukamin akanta da matakin albashi na 14.

Hazalika, ni ma ina aiki, ka ga muna samun albashin da muke rike kanmu, sannan daga babban gida ya fito.

Ka dubi gidan da muke zaune a ciki, ka san muna rayuwa ta rufin asiri.”

‘Yadda ya kashe kansa a ranar’

Matar marigayin ta ce, ba za ta manta da wannan bakar rana da lamarin ya faru ba, domin kamar yadda ta ce, a waccan ranar ce wani mutun ya zo ya yi wa mijinta sallama.

Da aka gaya masa cewa yana barci, sai ya tsananta cewa lallai a tayar da shi domin yana son ganinsa.

Hakan ya sa tilas ta je ta tayar da shi daga barcin. Bayan ya je wajen mai sallamar ya dawo dakinsa sai ya kira ta inda ya nemi ta kawo masa kayansa da ta wanke, ya sanya su ba tare da an goge su ba.

Hatta abincin karin kumallon da ta kawo masa bai tsaya ya ci ba, sai ya ce mata sai ya dawo wajen karfe 2:00 na rana.

Ta ce “Da na ga har karfe 3:00 bai dawo ba, kuma ga shi ba ni da waya a hannuna balle in kira, sai na yanke shawarar zuwa gidanmu in ga ko yana can.

“Kwatsam, sai na ga taron jama’a ana ta koke-koke, a can na ji abin da ya faru.”

‘Yana kula da mu’

Malama Hadiza ta ce, lallai akwai bakin cikin mutuwar miji ga matarsa wadda suka kwashe tsawon shekara 20 tare.

A cewarta, abin da ta fi jin bakin ciki shi ne, ba ta san wanda ya zo ya yi wa mijinta sallama har suka tafi ba, sannan ba ta san dalilin da ya sa mijinta ya kashe kansa ba.

“Bayan an sanar da ’yan sanda a Daura sun zo sun dauki gawar aka yi mata jana’iza kamar yadda addini ya tanada.

“Duk da halin bakin cikin da kowane lokaci yake ciki, hakan bai hana shi ba mu kyakkyawar kulawa ba,” inji ta.

Kafin faruwar lamarin wani daga cikin mutanen garin ya ce, a wannan rana ta Lahadi, ya ga Kawu a cikin motarsa ya nufi hanyar garejin gyarar mota, har ma ya tambaye shi ko gyara zai kai motar, ya ce masa a’a, sai bai sake ce masa uffan ba, ya wuce.

Makonni biyu da suka gabata ne Aminiya ta ruwaito cewa, marigayi Kawu ya kashe kan shi ta hanyar rataya.