Dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa a jam’iyyar LP, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya zubar da hawaye lokacin da ake tsaka da muhawara a gidan talabijin.
Ya zubar da hawayen ne lokacin da yake korafi kan yadda ya ce ’yan adawa na zagin ’yan gidansu, musamman ma mahaifinsa.
- Matsin tattalin arzikin da duniya za ta fada a 2023 zai zarce na 2022 — IMF
- 2023: Dalilina na janyewa daga takarar dan majalisa — Alan Waka
Lamarin ya faru ne yayin shirin tattaunawa da ’yan takarar Shugaban Kasa kai tsaye da gidan talabijin na Channels ya shirya ranar Lahadi.
Yusuf Datti ya kuma bayyana abin da ya ce ya yi wajen dakile masu sukar lamirinsa da kuma abokin takararsa, Peter Obi.
Ya ce, “Lokacin da na shiga takara tare da Peter Obi, na kori wasu karairayi a kansa, musamman daga ’yan APC.
“Lokacin da mutane suka fara tunanin suna da kudi, suna da mulki, giyar mulkin takan Buhari da su. Idan haka ta faru, dole sai an sami wani ya taba su a kafada. Da suka yi min, sai na mayar da martani don ni ba na jiran ko ta kwana.
“Sai suka daina. Sai dai yanzu sun koma kaina da na ’yan uwana saboda kokarin da muke yi ma ceto Najeriya.”
Yusuf Datti ya kuma ce idan da ma iya shi kadai ake suka da da sauki, amma har iyayensa sai da aka taba.
Ya ce, “Kusan shekara 35 ke nan da mahaifina ya rasu, Allah Ya jikansa. Ba a taba zaginsa a gabana ba sai da na tsaya takarar Mataimakin Shugaban Kasa. Wannan sam babu adalci a ciki kuma duk duniya babu inda ake haka sai Najeriya.
“Bai kamata ka rika zagin iyayen mutum ba,” inji shi, yayin da ya ci gaba da share hawayen har ya bar dakin taron kafin ya sake samun natsuwa ya dawo.