A makon jiya ne Kungiyar Ci-gaban Yankin Funtuwa da ke Jihar Katsina, ta yi wani gagarumin aiki inda ta tallafa wa mutanen yankin sama da 100 da kudade don gudanar da hidimar Babbar Sallah. Wakilinmu ya tattauna da Shugaban Kungiyar kuma Limamin Masallacin Gidajen ’Yan Majalisar Wakilai da ke Zone B, Apo, Abuja, Imam Ibrahim Awwal (Usama) don jin abin da ya karfafa wa kungiyar gwiwar yin wannan aiki da kuma ayyukan da kungiyar ta sanya a gaba:
Me ya karfafa muku gwiwar kafa wannan kungiya kuma mene ne ayyukanta?
Babban abin da ya karfafa mana gwiwar kafa wannan kungiya shi ne domin kare mutuncin al’ummarmu tare da tallafa musu ta hanyoyi da dama. Shekara daya ke nan da kafa wannan kungiya. Kuma Sanata Abu Ibrahim daga Jihar Katsina da dan Majaisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Funtuwa Alhaji Mukhtar Dandutse da Malam Hassan Idris da ni, muka tsaya wajen kafa wannan kungiya. Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya kaddamar da ita a Abuja. Kuma dubban mutanen yankin suka halarci kaddamar da kungiyar.
Wadanne ayyuka kungiyar ke gudanarwa?
Ayyukan da wannan kungiya ta sanya a gaba sun hada da kula da mutanenmu masu rauni kamar marayu. Muna son mu gina gidan marayu da makaranta da asibiti, domin mu rika tallafa musu muna daukar nauyinsu. Bayan haka za mu tallafa wa guragu da kafafuwan roba. Akwai wadansu mutanen Indiya da muka yi magana da su kan wannan aiki. Haka kungiyar za ta dauki nauyin yi wa masu ciwon ido aiki kyauta.
Muna da bangarori da dama a wannan kungiya kamar bangaren lauyoyi, muna da su a Abuja da Katsina. Idan kana cikin wannan kungiya wata shari’a ko rikici ya same ka, in har kana da gaskiya za su tsaya su kwato maka hakkinka.
Muna da bangaren kiwon lafiya wanda nan gaba idan kana da katin shaidar dan kungiyar za ka rika samun magani kyauta. Kuma muna da burin gina kananan asibitoci don amfani ’ya’ayn wannan kungiya. Kuma za mu gina makaratun yaki da jahilci don karantar da ’ya’yan wannan kungiya.
Daga kafa wannan kungiya zuwa yanzu wadanne nasarori kuka samu?
Babbar nasarar da muka samu ita ce wannan gagarimin aiki da muka yi na tallafa wa jama’r yankin Funtuwa da kudade don gudanar da hidimar Babbar Sallah. Ganin halin da ake ciki na matsin rashin kudi, ya sanya wannan kungiya ta kudiri yin wannan aiki don wadanda aka tallafawa su gudanar da dawainar wannan Babbar Sallah cikin sauki.
A karkashin wannan shiri akwai wadanda aka bai Naira dubu hamsin-hamsin akwai wadanda aka su Naira dubu talatin-talatin akwai wadanda aka ba su Naira dubu goma-goma. Sama da mutum 100 ne suka samu wannan tallafi. Kuma mun tura wa mutanen tallafin kudaden ne ta asusun ajiyarsu na bankuna da suka ba mu. Uban wannnan kungiya Mai girma Sarkin Maska Hakimin Funtuwa Alhaji Idris Sambo Idris da al’ummar yankin sun yaba da wannan kokari da wannan kungiya ta yi. Bayan haka mun samu nasarar samar wa matasan wannan yanki ayyuka da dama a wurare daban-daban.
Mene ne babban burinku?
Babban burinmu shi ne mu fitar da mutanenmu daga cikin kuncin rayuwa, muna son muga mutanenmu suna cikin walwala da jin dadi.Kuma muna son mu gina yankinmu
Ko a akwai tallafin da kuke samu daga wasu mutane don gudanar da ayyukanku?
Gaskiya lokacin da muka kaddamar da wannan kungiya, Honorabul Muntari Dandutse ya ba mu kekunan NAPEP uku. Wadannan Keke NAPEP an yi ta yin aiki da su ana tara kudin ana sakawa a asusun ajiyarsa, saboda lokacin ba mu bude asusun kungiyar ba. A takaice dai har zuwa wannan lokaci ba mu samu mun karbi wadannan kudade da ake tarawa ba.
Haka kuma Mai girma Sanata Abu Ibrahim ya bai wa wannan kungiya kyautar mota. Bayan haka duk fadin Jihar Katsina, babu wanda ya dauki ko kwabo ya ba mu. Amma kamar wannan aiki da muka yi na tallafa wa mutanen wannan yanki da kudaden hidimar Babbar Sallah, wadansu sanatoci da ’yan majalisa da wadansu muhimman mutane ne suka tallafa wa kungiyar.
Wane sako ko kira ne kake da shi ga al’ummar yankin?
Ina kira ga al’ummar yankin Funtuwa kan kowa ya yi kokari ya zo ya shiga wannan kungiya. Domin wannan kungiya ta zo ne don taimaka wa al’ummar yankin.