✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa Kungiyar ASUU ke yajin aiki –Dokta Sabo

Dokta Abubakar Sabo shi ne Shugaban Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta Jami’ar Usman Dan Fodiyo, Sakkwato. A tattaunawarsa da Aminiya, ya ce ba don san…

Dokta Abubakar Sabo shi ne Shugaban Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta Jami’ar Usman Dan Fodiyo, Sakkwato. A tattaunawarsa da Aminiya, ya ce ba don san ransu suke yajin aikin ba:

 

Kusan wata biyu ke nan kuna yajin aiki amma har yanzu ba ku samu matsaya da gwamnati ba, me ya sa?

Kamar yadda mutane suka sani yanzu mun fi wata biyu da shiga yajin aiki saboda alkawarin da gwamnati ta yi mana ba ta cika ba tun a shekarar 2013. Kowa ya san wannan alkawarin ya samo asali ne a shekarar 2002 muka koma 2005 da 2007 da 2009 a wannan lokacin ne marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa ya aminta da  yarjejeniyarmu, kafin ya sanya hannu ya bar duniya. Mun fadi hanyoyin da za a bi a tallafa wa jami’o’in kasar nan. An yi ta yi mana alkawarin za a ci gaba da aiwatar da su a 2010 da aka kasa cika alkawarin muka sake shiga yajin aiki a 2013. A nan ma muka sake zama da Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu ta yarda za a tallafa wa jami’o’i su cimma tsararsu na duniya. Abin mamaki duk shekarun nan ba a cika alkawarin da aka dauka ba mun yi ta shiga yajin aiki muna jawo hankalin gwamnati ta ki cika alkawarinta. Wannan yajin aikin da muka shiga ba sabo ba ne, ci gaba ne na wanda muka fara tun farko. Yanzu gwamnati ta kira mun yi ta zama da ita amma ba wani takamaimen abu a bangarenta da zai warware matsalar.

 

Mutane na ganin kuna shiga yajin aiki ne saboda son kanku, me za ka ce?

Eh to mafi yawan masu wannan magana ba su fahimci dalilan da suka sa muke shiga yajin aiki ba ne. Ya kamata mutane su sani duk jami’o’in duniyar nan babu jami’a daya a Najeriya da take shiga cikinsu a tsarin kayan aiki da wurin koyar da dalibai mai inganci. Hakkokin malamai ba a biya, wadannan abubuwa suna cikin abin da ake nema a samu a kasar nan. Shugaban zama na bangaren gwamnati Dokta Wale Babalakin ya ce ba dole ba ne sai gwamnati ta dauki nauyin ilimin yara, iyayensu su dauka, a sayar da jami’o’in kasar nan, in an yi haka yaro zai iya biyan dubu 500 ko miliyan daya a zangon karatunsa. Mun tambaya yaya za a yi iyaye su samu kudin, sai ya ce a kirkiro bankin ilimi, wannan banki zai rika ara wa dalibai kudi, in yaro ya kammala karatu a karbe takardunsa in ya samu aiki ya biya a mayar masa da takardunsa. A nan muka fahimci wannan mutum yana da ra’ayin a ci amanar ’ya’yan talakawa kuma ra’ayinsa ya saba wa tsarin mulkin kasar nan. Nan muka ce sai an cire shi, shi ne abin da ya kara wa tattaunawar zafi. Mu ba mu bukatar karin albashi, ba mu taba yajin aiki don albashi ba, sai don hakkokinmu da son inganta jami’o’inmu. Mun dauki alkawarin bai wa yara ilimi mai inganci dole ne mu shiga yajin aiki don ba mu iya cika alkawarin ga shi kuma gwamnati ta ki mayar da hankali kan ilimi sai wasu abubuwa da ba su kai amfanin ilimin ba.

 

Me kake ji ya sa mutane ba su fahimtarku kamar sauran kungiyoyi?

To su sauran kungiyoyi ra’ayinsu ne suke karewa na karin albashi. Jama’a na da wannan fahimtar musamman abin da ya shafi kudi, mu ko kungiya ce da ta shafi masu ilimi, kuma ba maganar karin albashi abin da zai ceto al’umma daga halin da suke ciki ya dame mu. Mun auna halin da karatunmu yake da ci gaban duniya, mun ga muna baya sosai. Don haka dole mu nemo wa kanmu mafita. Kashi 80 na malaman jami’a ba su iya kai yaransu kasar waje su yi karatu daga albashin da suke karba, ba mu da wani wurin da yaranmu ke karatu sai nan. Wani abu da ba ka sani ba kashi 80 na nasarorin da jami’o’in suka samu ya samu ne kan yajin aikin da muke shiga domin gwamnati ba ta gane komai sai wannan.

 

In aka dubi jami’o’in kasar nan suna da gine-gine da Asusun Kula da Manyan Makarantu ya samar, ba ku ganin wadannan a matsayin ci gaba?

Ai wannan asusun ba da lallami aka yi shi ba sai da muka yi yajin aiki aka samar da shi don gwamnati ta ce ba ta da kudi muka fada mata hanyar da za a bi a samu kudin. A lokacin da aka kirkiro shi a matsayin asusun ilimi, haraji ne aka rika dora wa wasu kamfanoni da ke samun kudi, a cire wani kaso na haraji muka ce a raba. Makarantu jami’o’i ne kawai suka yi yajin aiki amma asusun aka sanya kwalejojin ilimi da na kimiyya da kere-kere, sai muka aminta domin ci gaba muke bukata. Amma ina tabbatar maka ita kanta TETFUND din an siyasantar da ita, ba aikin da ake so take yi ba ana kawo wani abu da yake kawo matsala ga ilimi don ’yan siyasa na tsoma hannunsu. Yanzu ko assasa jami’a an siyasantar da shi, an kirkiro sababbi bayan an kasa inganta wadanda muke da su. Ina amfanin gini babu kayan aiki da bincike na zamani? A doka bai wuce in karantar da yara 50, amma ina karantar da dalibai dubu biyu ko fiye, don haka ya kamata a biya ni saboda karin aiki, amma ba a biyanmu. Kudin da muke nema  Naira tiriliyan daya da biliyan 200 ne na inganta ilimi, ba mu ce a ba mu lokaci daya ba, a kawo tsari da kudin za su rika fita har a fitar da su gaba daya. A rika ba ilimi kaso 26 a kasafin kudi. Tun 2011 da ya samu kaso 11 bai sake samun ko kaso10 ba.