✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa farashin manja ke hauhawa —Manoma

Najeriya kasar jari-hujja ce. Manoma na kuka, suna neman a ba su rance.

Wasu manoman kwarar manja da sarrafa shi sun jingina tashin farashin manjan ga karancin tallafi daga gwamnati da kuma hana shigo da shi daga kasar Indonesiya.

Da yake yi wa Aminiya bayani, wani manomin kwarar manja a Jihar Edo, Mista Peter Agwele, ya ce dalilai da yawa ne suke haddasa tashin farashin manja a Najeriya.

“Karuwar masu bukata da karancin abin da ake samarwa shi ke sa farashin kayayyaki ciki har da manja ya tashi.

“Yayin da mabukata suka yi yawa kuma kaya ya yi karanci, to dole farashinsa ya yi sama.

“Sauran dalilan sun hada da yakin Rasha da Ukraine wanda ya taba kusan komai da ya shafi mai,” inji shi.

Ya ce, Najeriya tana daya daga cikin kasashe masu shigo da manja, wanda bayan kasar Indonesiya ta hana fitar da shi zuwa wasu sassa na duniya hakan ya shafi Najeriya kuma ya tilasta tashin farashinsa.

Ya ce, Jihar Edo na shirin yin hadaka da Babban Bankin Najeriya (CBN) don bunkasa noman kwarar manja da bunkasa samar da manjan.

Manomin ya ce, kashi 60 zuwa 70 na masu samar da manja, kananan manoma ne wadanda ba za su iya janyo hankalin gwamnati da cibiyoyin kudi wajen samun tallafin kudi ba.

Ya ce iya abin da suka mallaka kawai za su yi amfani da shi wanda a koyaushe bai isa.

Wani manomi, mai suna Harrison Okpaluwa, ya danganta tashin farashin manjan da hauhawar farashin Dala da ya shafi duk wani abu.

“Harkar samar da manja na bukatar jari mai yawa don inganta nomawa da sauran dawainiya ta leburori, wanda hakan na matukar cin kudi mai yawa,” inji shi.

Ya ce, hanya mafi sauki da gwamnati za ta shigo cikin harkar ita ce ta samar da tsaretsare tare da tabbatar da an yi aiki da su, ta yadda za su rika tafiyar da lamarin yadda ya kamata a abin da ya shafi samar da manja a Najeriya.

Ya ce, “Gwamnatoci a baya sun samar da dokoki da dama sai dai matsalar rashin bibiya da karanci ko rashin taimako daga bangaren gwamnati kamar yadda ake yi a wasu kasashe don taimaka wa kananan manoma ne ke kawo matsala.”

Ya koka kan yadda Gwamnatin Jihar Edo ke karfafa gwiwar manyan manoma ba tare da la’akari da kananan manoma ba, inda ya ce Bankin CBN da sauran kungiyoyi masu taimakawa ba sa taimakon lamarin.

Ya ce kamata ya yi gwamnati ta samar da dokokin da za su rika lura da yadda za a rika taimaka wa kananan manoma ta hanyar samun basussuka don lamarin ya sauya.

“Idan kananan manoma za su rika samun rance to za a samu karuwar manjan kuma farashinsa zai sauka.

“Najeriya kasar jari-hujja ce. Manoma na kuka, suna neman a ba su rance, amma an gwammace a bai wa manoma ’yan siyasa don su azurta kansu.

“Idan adadin abin da ake samarwa ya karu, dole farashinsa ya yi kasa, amma in bukatarsa ta yi yawa fiye da wanda ake samarwa, to dole farashinsa ya ci gaba da hauhawa,” inji shi.

Aminiya ta gano cewa, farashin manja a kasuwa ya danganta da yanayin kasuwar, inda jarka mai lita 20 ta manja ake sayar da ita daga Naira dubu 21 zuwa dubu 23 a yawancin jihohin Kudu, yayin da a jihohin Arewa yake kamawa daga Naira dubu 27 zuwa dubu 30.

A bara an sayar da jarkar manja mai lita 20 a kan Naira dubu 18 zuwa dubu 20 a Arewa, wanda kuma ya dara yadda ake sayarwa a jihohin Kudu