✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa EFCC ta gayyace ni – Kwankwaso

Kwankwaso ya ce shi ne ya kai kansa ba kama shi aka yi ba.

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya musanta labarin da ake yadawa cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta kama shi.

Ya ce sabanin yadda ake yamadidin cewa kama shi aka yi, shi ne ya kai kansa ofishin hukumar don ya wanke kansa daga zarge-zargen da ake yi masa kan karkatar da wasu kudaden ’yan fansho lokacin da yake mulkin jihar.

Kwankwaso, wanda tsohon Ministan Tsaro ne ya bayyana karar a matsayin wacce aka saka siyasa a ciki, wacce ya zargi abokan adawa da hannu a ciki a kokarinsu na shafa masa kashin kaji.

Ya ce sam babu kamshin gaskiya a zarge-zargen.

“Labarin cewa an kama ni karya ne kuma ba shi da tushe. A matsayina na dan kasa mai bin doka, ni ne da kaina na ziyarci hukumar ranar Asabar don na wanke kaina daga zarge-zargen da ake yi min.

“Na hadu da jami’an hukumar ta EFCC inda na shaida musu cewa na zo ne na wanke kaina kan tuhumar da ake da ita a kaina tun shekarar 2015, kuma na amsa dukkan tambayoyin da suka yi min,” inji Kwankwaso.

A kunshin tuhumar dai, ’yan fanshon sun zargi Kwankwaso da bayar da umarnin yin amfani da kudadensu lokacin yana gwamna wajen aikin gina gidaje wadanda aka ce don su aka yi.

Rukunin gidajen da aka gina guda uku dai a lokaci an sanya musu sunan Kwankwasiyya da Amana da kuma Bandirawo.