Jagoran Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) Farfesa Ango Abdullahi ya ce bai gayyaci ’ya’yan kungiyar zuwa bikin cikarsa shekara 80 a duniya ba, shi ya sa ba su halarta ba. Duk da haka an ga fuskokin kadan daga cikinsu da suka hada da Dokta Hakeem Baba Ahmed da Dokta Janaidu Mahammed sai kuma Shariff Ahmed.
Taron wanda ya gudana a gidan gonarsa na Arewa Confectoinarics da ke Basawa Zariya a ranar Asabar, ya samu halartar tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo wanda shi ne babban bako.
Da yake jawabi, Cif Olusegun Obasanjo ya ce Najeriya na fama da rashin tsaro da ayyukan ta’addanci da suka hada da kashe-kashen bayin Allah da sace mutane. Ya ce, wani abin ban takaici shi ne yadda aka sace wadansu ’yan tagwaye a lokacin da za su yi bikin aurensu a Jihar Zamfara inda ya ce bai kamata a sanya ido haka na faruwa ba.
Cif Obasanjo ya kuma shawarci Farfesa Ango Abdullahi wanda aka yi taron dominsa da ya kwance kayan da ya daura na kame bakinsa ko bayar da gudunmawa don ci gaban kasa. Ya ci gaba da cewa an san Farfesa Ango Abdullahi da tsayawa kan turbar fadin gaskiya a duk lokacin da ya ga al’umura na komawa baya musamman al’ummominsa da kasa baki daya.
Saboda haka sai ya shawarce shi ya ci gaba da yi wa kasa aiki domin shekara 80 ba karshen rayuwarsa ke nan ba.
Da yake jawabi, Farfesa Ango Abdullahi Magajin Rafin Zazzau ya ce ya zabi ya kasance cikin gwagwarmayar neman ’yancin al’umma tare da kawo sauyin shugabanci da zai tabbatar da hadin kan kasa ba wai a raba kan mutane ba.
Ya ce, lokaci ya yi da zai koma gefe don matasa su dora daga inda ya tsaya, amma hakan ya kasa samuwa saboda yadda suke tafiyar da gwagwarmayar ba zai yiwu su bar wa matasa ba har sai sun kammala gogewa.
Ya jawo hankalin matasa su nemi ilimi domin ta haka ne za su iya zama wani abu a nan gaba kamar yadda suke sha’awar Farfesa Ango. Haka ya ce matasa su rika mutunta juna tare da girmama ra’ayoyin juna ta haka ne za su samu zaman lafiya da ci gaba mai ma’ana.
Fafesa ya ce bai raba gayyata ba, don haka ya sa wadansu daga cikin abokansa ba su halarci taron nasa ba, kuma wadansu sun yi tafiya zuwa kasashen waje.
Sai dai ana ganin rashin halartar abokan gwagwarmayarsa na Kungiyar Dattawan Arewa kamar su Alhaji Sani Zagon Daura da Manjo Janar Paul Tarfa da su Kyaftin Bashir Sodangi da Ministan Matasa Saloman Dalung ba ya rasa nasaba da rabuwar kai da kungiyar ta samu kan shelar da Farfesa Ango ya yi cewa kungiyar ta janye goyan bayanta ga sake zaben Shugaba Buhari a 2019, wadda hakan ya bata wa wadansu da dama daga cikin su rai.