✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa Dala ta sake tashi zuwa N485

Darajar Naira a kasuwar canji ta bayan fage ta sake karyewa zuwa N485 a kan Dala daya a ranar Talata duk da cewa Babban Bankin…

Darajar Naira a kasuwar canji ta bayan fage ta sake karyewa zuwa N485 a kan Dala daya a ranar Talata duk da cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) na ba da Dala ne a kan N410.

Aminiya ta gano cewa duk da umarnin CBN na hukunta masu boye Dala domin karya darajar Naira, ’yan canjin bayan fage ba su daina boyewa ba.

Shugaban Kungiyar ’Yan Canji Masu Lasisi ta Kasa (ABCON), Aminu Gwadabe, ya dora laifin karyewar darajar Naira a kan ’yan canin bayan fage da masu boye ta don a samu karancinta, farashinta ya tashi.

Ya ce nan gaba, ’yan canji masu lasisi ne kadai za ta rika ba wa Dala kuma, “’Yan canji masu lasisi ba za su zura ido wa masu hasashen karyewar Naira da ’yan bumburutu su bata musu harka ba.”

Wasu dillalai kuma sun dora laifin a kan karancin bayar da Dala da karba-kabar rabon ta yayin da ake da matukar bukatar ta.

Sai dai Gwadabe ya ce ’yan canji masu lasisi za su ci gaba da mara wa CBN baya wajen tabbatar da bin dokar hana safarar kudade da yakar masu daukar nauyin ’yan ta’adda da kuma daidaiton darajar Naira.

Ya ce wajibi ne kamfanonin canji su samu ilimin gabatar wa hukumomi rahotonsu na canjin kudi, safarar kudadde, da kuma ajiye bayanan cinikinsu a kowane mako a kan lokaci ga CBN, hukumar EFCC da sauran hukumomi domin tantancewa.

“Ku rika hattara a harkokinku saboda a kowane lokaci jami’an CBN na iya zuwa su yi musu binciken ba-zata.

“Kowane kamfanin canji ya nada jami’in tabbatar da bin ka’ida da adana bayanai kamar yadda CBN ya ba da umarni wanda kuma shi ne tsarin da duniya ta aminta da shi.

“Sannan ku guji sayar da Dala fiye da farashin da aka kayyade, ko ba da rahoto a makare,” inji shi.

Gwadabe ya ce da bin dokokin, ’yan canji za su zama kyakkyawan abin koyi kuma za su karya gwiwar masu zuwa neman canji a kasuwar bayan fage.

A baya-bayan nan, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce an bullo da dokar cajin ‘N4 a kan cinikin kowace $1’ domin tabbatar da gaskiya da yin komai a fili a harkar canji.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa hakan zai ba wa bankuna da cibiyoyin hadahadar kudade damraar bullo da sabbin hanyoyin zuba jari da za su jawo hankalin ‘yan Najeria da ke kasashen waje.