✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa ban koma Najeriya ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce abin da kawai yake jira domin ya dawo Najeriya shi ne amincewar likitocinsa da suke Landan. Ya ce lafiyarsa…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce abin da kawai yake jira domin ya dawo Najeriya shi ne amincewar likitocinsa da suke Landan.

Ya ce lafiyarsa ta yi matukar inganta.

“Na koyi bin umarnin likitocina, maimakon in zamo mai ba da umarnin. A nan likitocin ne suke da iko,” Buhari ya shaida wa ayarin masu kula da harkokin watsa labaransa da suka je Ingila domin ganinsa.

Ayarin a karkashin jagorancin Ministan Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed, ya kuma kunshi Mai taimaka wa Shugaban kasa kan Harkokin Watsa Labarai Mista Femi Adesina da Babban Mai taimaka wa Shugaban kasa kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Garba Shehu da Mai  tallafawa kan Harkokin sadarwar Intanet, Misis Lauretta Onochie da Babban Mai taimaka wa Shugaban kasa kan Harkokin ’yan Najeriya mazauna kasashen waje, Hajiya Abike Dabiri-Erewa.

Shugaba Buhari ya ce hakika yana son dawowa gida, kamar yadda Adesina ya fadi a wata sanarwar intanet.

Ya ce, “Lokacin da ayarin suka nuna farin cikinsu kan ingantuwar lafiyar Shugaban kasar, sai ya amsa da cewa; “Ina jin shaukin dawowa gida, amma likitoci ne ke da iko a kan haka. Yanzu na koyi biyayya ga umarnin likitoci maimakon a yi min biyayya.”

Da aka tambaye shi yaya yake ji game da mabambantan ra’ayoyi game da batun lafiyarsa, Shugaba Buhari ya yi murmushi sannan ya ce yana bibiyar abubuwan da suke faruwa a gida sau-da-kafa.

Ya yaba wa gidajen talabijin na Najeriya da sauran kafafen watsa labarai, kan yadda suke sanar da shi bayanan abubuwan da suke faruwa a kasar nan.

Da aka shaida masa cewa jama’a na ci gaba da yi masa addu’o’i ba ma a Najeriya kawai ba har da sassan kasashen Afirka da duniya, sai aka ruwaito shi yana cewa: “Abin da muka yi a kasar Gambiya a farkon bana, ya jawo mana dimbin fatan alheri a Nahiyar Afirka. Ya kara mana martaba. Kuma ina godiya ga dukan wadanda suke yi addu’ar. Allah Ya saka musu da alheri.” 

A cikin sanarwar Shugaba Buhari ya mika godiya ga daukacin ’yan Najeriya, inda ya bayyana fatan kasancewa tare da su cikin kankanen lokaci.

Shugaba Buhari ya bar Najeriya ne a ranar 7 ga Mayun bana don sake ganin likitocinsa a Ingila.