Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce takaddamar wanda zai yarda ya zama Mataimaki ce ta rusa batun kawancensa da dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi.
Kwankwaso ya ce dalilin da ya sa ya ki amincewa ya karbi mukamin mataimaki shi ne muddin ya yi haka, to jam’iyyarsa ta NNPP za ta iya mutuwa.
- Tella: Kasuwar da ake cinikin sama da shanu 3,000 a rana daya
- Kiristoci sun taya Musulmi sharar masallacin idi a Kudancin Kaduna
Dan takarar, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne ya bayyana haka ne a Gombe yayin hirarsa da manema labarai, lokacin da ya ziyarci Jihar domin kaddamar da ofishin jam’iyyar a Jihar.
Ya ce tarin kwarewa da gogewar da yake da ita sun taimaka wajen ganin jam’iyyar ta sami karbuwa cikin kankanin lokaci.
Dan takarar ya ce la’akari da irin karbuwar da NNPP ta samu, duk wani abin da ta samu in ba takarar ta Shugaban Kasa ba zai iya sa wa ta wargaje.
Kwankwaso ya ce, “Daga tattaunawar da muka yi da jam’iyyar Labour, babban kalubalen shi ne na wanda zai zama dan takarar Shugaban Kasa idan kawancenmu ya tabbata.
“Daga karshe wasu daga cikin wakilanmu suka amince cewa dole a yi la’akari da wasu abubuwa kamar shakaru, kwarewa, mukaman da mutum ya taba rikewa a baya, cancanta da kuma jajircewa da sauran abubuwa.
“Tabbas su daya bangaren ba za su so hakan ba. Yawancinsu sun yi amannar cewa dole Shugaban Kasa ya fito daga can (Kudu maso Gabas).
“Idan na amince na zama dan takarar Mataimaki, jam’iyyarmu ta NNPP za ta rushe, saboda diga-diganta na kan abubuwan da muka shafe shekara 30 muna ginawa.
“Na yi shekara 17 ina aikin gwamnati, magana ake ta sama da shekara 47 ke nan a yanzu, wannan shi ne ginshikin da ke rike da NNPP,” inji Kwankwaso. (NAN)