Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana riko da tsarin nan na “safe school initiative” a matsayin sirrin da ya sa ba cika samun labarin satar ‘yan makaranta ba a jihar.
Tsarin na “safe school initiative” dai wani shiri ne da ya wajabta gina katanga da daukar ma’aikata masu ɗauke da makamai domin kare lafiya da dukiya a makarantu.
Zulum ya bayyana ne Fadar Gwamnatin Najeriya jim kaɗan bayan fitowarsa daga wani taro na shuwagabanni a kasar nan.
Zulum ya ce “Mun kai akalla shekara bakwai zuwa takwas da ƙaddamar da tsarin ‘Safe School Initiative ’ a Jihar Borno.
“Kusan duk makarantunmu na da katanga, mun gayyaci sojoji da ’yan sanda aikin tsare ɗalibai da makarantunmu.”
- Yadda gayyatar da jami’an tsaro suka yi min ta gudana — Sheikh Gumi
- Dalilin da ya hana ’yan Najeriya da dama samun bizar Umarah — Hukumar Alhazai
Zulum ya kara da cewa “Mun ɗauki ’yan banga da ’yan sa-kai suna taimaka wa jami’an tsaron kasar nan yadda ya kamata wurin tabbatar da tsaro a makarantun Jihar Borno.”
Gwamna Zulum ya jinjina wa jami’an tsaron bisa ƙoƙarin da ya ce suna yi wurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Borno da sauran sassan kasar nan.
Jihar Borno dai ɗaya ce daga cikin jihohin da suka sha fama da bala’in ta’addancin kungiyar Boko Haram da ISIS masu tada ƙayar baya.