A karon farko Shugaba Buhari ya kare gwamntaninsa kan karin farashin man fetur da wutar lantarki, wanda ’yan kasa musamman jam’iyyun adawa da masu sharhi suka yi ta suka.
Buhari ya ce tasirin annobar COVID-19 ga tattalin arzikin kasashe a fadin duniya ce ta sa gwamnatinsa yin sauye-sauye ga manufofinta na dogon zango domin amfanin ’yan Najeriya, duk da cewa da farko ba za a ji dadin hakan ba.
- Shugabanni su guji neman dawwama ka kan mulki —Buhari
- Auren Hanan: Aisha Buhari ta fusata da zanen barkwanci
- Ruwan kudi a bikin auren diyar shugaban kasa na shan caccaka
“Kuna sane da cewa farashin mai ya karye a lokacin dokar kulle a duniya, don haka muka cire hannu a farashin fetur domin masu saye su samu saukin farashi, wanda kowa ya yi na’am da shi.
“Abin da hakan ke nufi shi ne farashin zai rika sauyawa gwargwadon yadda kasuwar danyen mai take a duniya. Wato farashin zai karu idan farashin danyen ya samu tagomashi”, inji shi.
– ‘Ba mu da zabi’ –
A jawabinsa ga taron bitar ayyukan gwamnatinsa a shekarar farko ranar Litinin, Buhari ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa duk da cewa babu tanadin tallafin mai a sabon kasafin 2020, gwamnati ba za ta kyale ’yan kasuwa su kara farashin mai barkatai ba.
Ta bakin Mataimakinsa Yemi Osibanjo, shugban ya ce illar gwamnati ta kayyade farashin mai shi ne za ta biya tallafi, wanda ka iya jawo karancin man.
“Yanzu kudaden shigarmu sun ragu da kashi 60%, don haka ba za mu iya biya ba.
“Na biyu shi ne yiwuwar dawowar dogayen layuka a gidajen mai, wanda ya zama tarihi a karkashin wannan gwamnti. ’Yan Najeriya ba sa wahalar bin dogayen layin sayen mai da yawanci aka yi wa kari fiye da kima.
“Sannan ba a yi wa tallafin mai tanadi a kasafin 2020 saboda ba za mu iya ba, idan har za a ba da kaso mai tsoka ga bangaren lafiya, ilimi da sauran bukatu. Ba mu da zabi”, inji Osinbajo.
– Ba za mu kyale ’yan kasuwa ba –
Ya ci gaba da ce, “yanzu aikin da ke gaban gwamnati shi ne hana ’yan kasuwa kara farashi barkatai da cutar ’yan kasa. Shi ya sa hukumar lura da farashin mai (PPPRA) a kwanakin baya ta sanya mizanin da gidajen mai ba za su wuce ba.
“Amfanin da aka samu yanzu shi ne kowa na iya kawo mai ya yi gasa da ’yan kasuwar, wanda hakan na iya sa su rage farashin”, inji Osinbajo.