Kusan mako biyu rikicin shugabancin da ya kai ga wani tsagi sanar da korar Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano, daga karshe malamin ya yi tsokaci a kan rikicin.
Ya bayyana rikicin a matsayin wata jarrabawa daga Allah don ya jarraba imaninsu.
- An kama yaro mai shekara 14 a cikin ’yan bindigar Katsina
- Ya biya ’yan bindiga su yi garkuwa da mahaifinsa
Sheikh Khalil na bayani ne a Kano ranar Asabar, lokacin da ya karbi bakuncin Majalisar Tabbatar da Shari’a a Najeriya da ta kai mishi ziyarar goyon baya a sakatariyar majalisar.
Aminiya ta rawaito cewa wani bangare na Majalisar Malaman ya sanar da dakatar da Sheikh Khalil daga shugabancinta, bisa zargin siyasantar da ita, tare da maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban riko.
Sai dai dakatarwar ta bar baya da kura inda wasu bangarorin malaman suka ce ba a tuntube su ba, don haka ba su amince ba.
To sai dai Sheikh Khalil ya ce, “Allah Ya yi alkawarin jarraba mu a kowanne abu. Abin da ya faru watakila Allah Ne Ya yi niyyar jarraba mu don Ya ga ko da gaske muke a tafarkinsa.
“Saboda haka, na dauki wannan a matsayin jarrabawa, amma Alhamdulillahi, Allah Ya nuna mana tsintsiya madaurinki daya muke, kuma ina rokon Ya yafe mana.
“Ina godiya ga dukkn wadanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin kan malaman Kano ya hadu, ciki har da wadanda ma ba sa cikin majalisar, amma suna mana fatan alheri,” inji Sheikh Khalil.
Tun da farko da yake jawabi a madadin Majalisar Tabbatar da Shari’ar, Malam Jamilu Mu’azu Haidar, ya ce sun zo Kano ne a madadin kungiyar ta kasa, don nuna goyon bayansu ga shugabancin nasa.
Malam Jamilu, wanda kuma mamba ne a Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musukunci ta Najeriya (NSCIA), ya ce sun saurari bayanai daga malaman Kano daban-daban, inda aka ba su tabbacin cewa babu hannun gwamnatin jihar a rikicin.
“Muna kira ga sauran malamai sa su ji tsoron Allah su dawo a ci gaba da tafiya tare, karkashin Sheikh Khalil, kamar yadda ake a baya,” inji Malam Jamilu.
Wadanda suke cikin tawagar sun hada wakilan Malisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, kungiyar Fityanul Islam da kuam Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS) daga sassa daban-daban na Najeriya.
Majalisar Malamai ta Jihar Kano ita ce kungiya mafi girma ta addinin Islama a jihar, inda ta tattaro malamai mabiya akidu da dariku daban-daban karkashin inuwa daya.