✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya hana Buhari ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda – Garba Shehu

Ya ce abin da gwamnati ta yi ya fi na ayyana su a ’yan ta’adda.

Babban mai taimaka wa Shugaban Kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya ce abin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi wa ’yan bindiga ya ma wuce na ayyana su a matsayin ’yan ta’adda.

Ya kuma musanta zargin da ake cewa gwamnatin na yin laku-laku wajen yakar ’yan ta’addan da suke kawo barazana ga tsaron kasa.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da Sashen Pidgin na BBC ranar Asabar.

A cewarsa, akwai umarnin da Shugaban ya bayar kan cewar duk dan bindigar da aka gani a harbe shi nan take, amma bai bayar da irin wannan umarnin a kan mambobin haramtacciyar Kungiyar ’Yan Awaren Biyafara ta IPOB ba.

Ya ce, “Shin kun san akwai umarnin Shugaban Kasa kan duk dan ta’adda ko dan bindigar da aka gani dauke da makami ko AK-47 a harbe shi nan take?

“Gaskiya ne an haramta kungiyar IPOB, amma babu umarni na kai tsaye cewa duk inda aka ga mambobinsu a harbe su. Babu wata hujja da za ta nuna cewa ana yi wa ’yan bindiga sako-sako.”

Malam Garrba ya kuma ce an sami matukar nasara a yaki da ta’addanci a Najeriya.

“Sojojin saman Najeriya na can na ragargazar su a maboyarsu, sojojin kasa kuma na binsu ta kasa, ba a raga wa ko sassauta musu ko kadan.

“Magana ce kawai ta lokaci, za mu kakkabe su gaba daya, kuma Najeriya za ta koma zaman lafiyarta kamar a baya.

“Alal misali, kullum mambobin Boko Haram yanzu suna nan suna mika wuya. Kafin Buhari ya karbi mulki, ’yan Najeriya da dama ba sa iya zuwa wuraren ibada ko kasuwanni ko tashohin mota da sauran wuraren taruwar jama’a,” inji shi.