Ambaliyar da ta auku a 2024 ita ce mafi muni a shekaru 30 da suka gabata a Maiduguri, fadar Jihar Borno.
Wannan ambaliya ta samo asali ne daga ruwan sama kamar da bakin kwarya ta da aka tafka na tsawon kwanaki a Maiduguri da akasarin kananan hukumomin Jihar Borno.
Maiduguri da yankin Jere na daga cikin wuraren da lamarin ya fi kamari, inda a ranar Litinin Gwamnatin Jihar Borno ta rufe makarantun firamare da sakandare domin kare dalibai daga salwanta.
Daga bisani, a ranar da dare, lamarin ya sanadiyyar fashewar Madatsar Ruwa ta Alau mai nisan kilomita 10 daga garin Maiduguri.
- Asarar da muka yi a ambaliyar Borno —’Yan kasuwa
- Ya kai wa ’yan sanda cin hancin N1.5 su sako ɗan Shi’a
ِA cikin dare ruwan ya fara mamaye unguwanni, inda kafin wayewar gari yawancin unugwannin garin suna cikin ruwa, a wani yanayi da shekaru 30 ke nan rabon da ga irinsa a garin.
Ambaliyar ta mamaye Fadar Shehun Borno, hadi da raba dubban mazauna unguwannin Post Office, Gwange, Moromoro, Gadar Customs, Gidan Zoo, Bulabullin, Maidoki Roundabout, Jami’ar Maiduguri, Cocin Saint Patrick da sauaransu da muhallansu.
Da talatainin dare ne ambaliyar ta mamaye Fadar Shehun Borno da tituna da gidaje da gadojin da sauran wurare, lamarin da ya tilasta wa jama’a sauya matsuguni.
Ya ce ruwan ambaliyar ya yi ƙarfin gaske inda ya mamaye Fadar Shehun Borno, Kofa Biyu, Gadar Fori wadda ta haɗa Fori da Galtimari zuwa Tashan Bama.
A cewarsa, unguwannin da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Fori, Galtimari, Gwange, da Bulabulin.
“Kowa ya kaurace wa yankin post office, kasuwar Monday Market zuwa zoo da gidan man Hissan saboda ambaliya ta riga ta shanye su, mota ba ya iya bi,” in ji Refeal.
“Da mislain 12:30 aka sanar da mu cewa mu kwashe ’yan kananan kayan da za mu iya, amma kafin mu ciro takardun shaidar karatumu, har ruwan ya kawo mana mara,’ in ji wani mazaunin Galtimari.
Bilyaminu Yusuf, ya ce, “muna cikin mawuyacin hali a Lagos Street, ambaliya ta sa mu hijira zuwa makarantar Firamare ta Galtimari mun bar kayanmu a gida.”
Wakilinmu ya gano yadda ruwan ya shanye Gadar Lagos Street, daya daga cikin manyan gadojin da ke garin Maiduguri.
Hakazalika gidan radiyo da talabijin na jihar (BRTV) Post Office, Shehu Laminu way, da unguwar Custom su ma ambaliyar ta shafe su.
Wani ma’aikacin BRTV ya wallafa a Soshiyal Midiya cewa, “ruwa ya shanye ofishinmu da Post Office.”
Kimanin mako guda ke nan da ambaliyar ta yi ƙamari a jihar, inda lamarin ya kai maƙura a safiyar Talata.
Kazalika ambaliya ta mamaye wurare da dama a Ƙaramar Hukumar Jere ta jihar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Borno ta bayar da umarnin rufe makarantun firamare da sakandare domin guje wa asarar rayukan dalibai a sakamakon ambaliyar.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne sakamakon rahoton da ke nuna yiwuwar ƙaruwar ambaliya a Maiduguri da Jere da wasu sassan jihar.
Asara a kasuwanni
Wani dan kasuwa ya ce, “Duk shagunan da ke Monday Market da Post Office ruwa ya shanye su.”
Wakilinmu a garin Maidurugi ya zagaya garin, inda ya iske ’yan kasuwar Monday Market suna lissafin irin asarar da suka yi sakamkon ibtila’in.
Wasu daga cikinsu sun nuna matukar kaduwarsu da kuma tunanin yiyuwar maye gurbin abin da suka rasa a ambaliyar.
Wani mai sayar da sukari da fulawa a kasuwar, Muhammad Bulama, ya ce ambaliyar ta shanye kasuwar gaba daya.
“Duk shagunanmu da ke kallon gidan Marigayi Alhaji Mai Sugar sun yi ambaliya, sukari da fulawa da shinkafa da kayan girki na miliyoyin Naira sun lalace.
“A sa mu a add’ua! Buhunan kayan abinci irin su sukari da shinkafa da gishiri da taliya da sauransu duk sun jike sun narke,” in ji shi.
Wakilinmu ya lura yawan ruwan da ke ambaliyar yana kara kaurwa inda yake kara shiga wasu unugwanni.
Hakazalika ambaliya ta mamaye Gidan Zoo na Kyarimi ta wuce da namun dajin da ke ciki, inda a halin da ake ciki namun dajin suke neman mafaka.
Wani mazaunin yankin ya ce, “yanzu haka mun fice daga unugwar saboda gudun hari daga namun daji da kwarin da ke gidan zoo.
Rundunar ’yan sanda a Jihar Borno ta bukaci jama’a da su kaurace wa yankunan da aka samu ambabaliya zuwa wasu wurare masu aminci.