✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya auku a Maimalari

Kwanton baunar da ake zargin ’yan Boko Haram sun yi wa sojoji, ya haifar da mutuwar soja hudu da suka taho daga Barikin Maimalari da…

Kwanton baunar da ake zargin ’yan Boko Haram sun yi wa sojoji, ya haifar da mutuwar soja hudu da suka taho daga Barikin Maimalari da ke Maiduguri a Jihar Barno, ranar Larabar makon jiya. Saboda fusatar da sojojin kan wannan asarar rayuka, ta sa suka huce haushinsu ta hanyar harbin kan mai uwa da wabi, inda suka yi nufin harbin Kwamandan runda ta bakwai, Manjo Janar Ahmed Mohammad, wanda daga bisani hukumomi suka bayyana cewa babu abin da ya same shi. Wannan runduna ta hada da Maimalari da hedkwatar rundunar sojojin yankin, wadanda aka tura don yakar masu ahrin kunar bakin wake. A kan hanyar sojoji ta komawa sansaninsu aka kai musu hari. Sojoji da dama sun jikkata.
Hukumomin soja sun yi taktsantsan wajen bayyana abin da ya auku a matsayin tawaye, sannan suka mayar da martanin nuna takaici kan wannan lakabi da kafafen yada labarai suka yi wa al’amarin da ya auku.
Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar tsaro, Majo Janar Christopher Olukolade ya bayyana cewa al’amarin ya auku ne a sanadiyyar mutuwar sojojin da ke dawo wa daga Chibok, inda aka sace ’yan mata ’yan makaranta fiye da 200 a fiye da wata guda da ya wuce. Ya bukaci kafafen yada labaran Najeriya da su daina kanbama matakin da sojojin suka dauka’ saboda al’amarin na iya mayar da kasar nan wuri mara kariyar tsaro ga kowa.
Rahotanni mabambanta kan al’amarin da ya auku, sun yi nuni da cewa hankali ya dungunzuma ne a lokacin da sojojin suka ga gawarwakin wadanda aka yi wa kwanton bauna aka kashe su. Sai al’amura suka rincabe da zuwan Manjo-Janar Ahmed Mohammed ya ziyarci barikin don yi wa sojojin jawabi. An ruwaito cewa ya yi tsawa ga wani soja, wanda ke tsananin nuna takaicinsa kan yadda ba a ba su managartan kayan aiki ba, da kuma fahimtarsa kan bayanan da aka yi musu game da mutuwar abokan aikinsu. Sai su ma sojojin da aka tara suka sai suka yi wa kwamandan tsawa, inda suka bukaci a bayyana musu dalilin da ya sa ba a bai wa abokan aikinsu managartan kayan aiki ba, kafin su suje su tunkari masu harin kunar bakin wake.
A yi ta samu jefa zargi a tsakanin kananan sojoji da aka tura don shawo kan hare-haren kunar bakin wake, kuma shugabanninsu da hukumomin soja na sane da cewa ba su da makamai masu inanci in an kwatanta su da masu ahrin kunar bakin wake da aka tura su, su fafata yaki da su. Wasu daga cikin zarge-zargen da sojojin Barikin Maimalari suka yi, sun hada da rashin makamai masu cin dogon zango, da rashin yanayin gudanar da aiki mai kyau da kin biyansu kudin alawus-alawus, da yanke musu kudin hakkokinsu ba bisa ka’ida ba, sannan an tsawaita yawan kwanakin da suka yi a wurin da aka tura su aiki da karin wasu watanni masu yawa. Sun kuma yi takaddama kan cewa wannan azawa da aka nuna ita ta kashe musu karsashin fafata yaki da ’yan tawaye.
Wannan al’amari da ya auku, shi yasa hukumar soja ta fara bincike. Sannan, an sake wa rundunar wani kwamandan. Hedkwatar tsaro ta yi takatsantsan wajen tantance matsalar Maimalari kafin ta fara gudanar da bincike. Tuni dai gwamnati ta bayyana cewa dawo da sojojin fagen fama, wani shiri ne na “kaddamar da yaki da ta’addanci.’
Matukar dai korafe-korafen da sojojin suka yi sun kasance gaskiya, to abin da ya auku a Maimalari na da matukar tayar da hankali. Me yasa aka yaudare su? Me yasa aka ajiye sojoji a wurin aiki na tsawon lokaci ba tare da an karbe su ba? Duk da dimbin kudin da ake ware wa harkar tsaro a kasafin kudi, me yasa sojojin ke kukan rashin managartan makamai?
Gwamnan Barno, Kashim Shettima, a wani lokaci can baya, ya taba bayyana cewa maharan Boko Haram suna da makaman da suka fi na soja; nan da nan fadar Shugaban kasa ta yi watsi da wannan bayani. Matakin da sojojin Maimalari suka dauka na tabbatar da wancan bayani da aka gabatar, kuma an nuna rashin daidaiton tsakanin bayanin da kwamandoji ke yi da na sojojin da aka tura fagen daga. Ko me ya haifar da hakan? Ya kamata kwamitin bincike da hukumar soja ta kafa ya binciko amsar wannan tambayar da ma sauran amsoshin tamabayoyin da aka sha bijiro da su.
Akwai bukatar Majalisar kasa ta gudanar da bincike, ba ma kan yadda al’amarin ya auku ba,  har ma ta binciki dimbin kudin da aka ware wa sojoji a ’yan shekarun da suka gabata, don a tantance gaskiyar lamari kan yadda ake amfani da kudin wajen yaki da masu tayar da zaune tsaye a kasar nan.