Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana damuwa kan zaman matasa babu sana’a a Najeriya yana mai kira ga gwamnati da ta samar musu da hanyoyin dogaro da kai.
Yayin jawabinsa na cikarsa shekara daya a sarautar Kano, Sarki Aminu Ado Bayero ya ja hankalin gwamnati da mawadata da sauran jam’a kan yadda kowannensu zai ba da gudunmuwa domin kyautata rayuwar al’umma.
- Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya cika shekara 1 a kan mulki
- ‘Maharan Dikwa ba yaren ’yan Najeriya suke ba’
- ’Yan bindiga: Rundunar Sojin Kasa ta gargadi Sheikh Gumi kan lafuzansa
- ’Yan sanda sun kama barayin yara a Bauchi
“Babban kalubale shi ne dukkaninmu mun san matasanmu da yawa ba sa komai — a zaune suke — kuma an san abin da irin wannan zama zai haifar ga al’umma gaba daya.
“Don haka muna kira ga gwamnati ta bijiro da wasu ayyuka musamman harkar noma da koyon sana’a wanda matasanmu za su dogara da kansu su kuma taimaka wa wadanda za su biyo bayansu.”
Sha’anin tsaro
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya kara kira ga ga al’umma su kasance masu hattara saboda kalubalen tsron da ke addabar Najeriya.
Ya kuma shawarce su da su su rika ba wa jami’an tsaro bayanai kan duk wani bakon ido ko take-taken da ba su aminta da shi ba.
“Ta haka ne za mu tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasarmu.”
Ya ce, “Ina kira ga jama’a da babbar murya da su yi hattara saboda wannan zamani mai cike da kalubalen tsaro. Muna addu’ar Allah Ya kare mu daga dukkan masu nufin cutar jama’a.”
Yaki da cutar coronavirus
Ya kuma bukaci jama’a da su ba da hadin kai ga yakin da Gwamantin Jihar Kano da ta Tarayya suke yi da cutar coronavirus sannan su karbi allurar rigakafinta.
“A ’yan kwanan nan an nuna Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Mataimakinsa suna karbar allurar rigakafin wannan cuta; muna kira ga mahukunta da su ci gaba da kokari don samar wa dukkan al’umma wannan rigakafi.
“Su kuma jama’a ina umartar su karbi wannan rigakafin duk lokacin da aka samar da ita bisa shawarar masana.”
Komawa ga Allah da zaman lafiya
Sannan ya ce, “Mu hada kanmu mu fahimci cewa dukkanninmu bayinSa ne da za su tsaya a gabanSa domin amsa [tambayoyi] kan dukkan abin da muka aiakata.
“Ina kira ga malamanmu da su dukufa wajen hada kawunan jama’armu, ba harkar rigima ba.
Taimakon talakawa
“Ga masu wadata muna kira gare su da su taiamaka wa marasa karfi a cikinmu.
“Haka magabatanmu suka yi suka ci nasara a rayuwa! Allah Ya kare mutuncinmu, Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya.”
“Wannan annoba da muke fuskanta Allah Ya yi mana maganinta. Iyayenmu da malamanmu da shguabanninmu da suka gabata Allah Ya jaddada musu rahama, Ya ci gaba da ba mu Albarka.
“Idan wa’adinmu ya yi, Allah Ya sa mu cika da imani.”