Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya girgiza bayan da ya yi masa bayanin irin aika-aikan da Gwamnatin Ganduje, wadda ta sauka kwananna ta aikata a jihar.
Kwankwaso ya kuma tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da Shugaban Kasa Tinubu game da ba shi mukamin minista a gwamnati mai ci.
Kwankwaso wanda shi da Ganduje suka gana a lokuta daban-daban da shugaban kasa a ranar Juma’a, ya ce Tinubu ya kowannensu su ne dambarwar rushe gine-ginen da sabuwar gwamnatin jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP take yi a jihar.
Bayan ganawarsa ne Kwankwaso ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa, Ganduje ya rushe ginin jami’ar jihar Kano, da yadda ya cefanar wa kansa da mukarrabansa kadoririn gwamnatin jiar ta barauniyar hanya.
- Tinubu ya dakatar da Gwamnan CBN Godwin Emefiele
- Da mun hadu da Kwankwaso da na dalla masa mari — Ganduje
Barnar da Ganduje ya yi —Kwankwaso
A cewarsa, akasarin filaye da gine-ginen da rusan da sabuwar gwamnatin NNPP ya shafa, Ganduje da mukararrabansa ne aka sayar wa ba bisa ka’ida ba.
Madugun na Kwankwasiyya ya kara da cewa a zamanin mulkin Ganduje, gwamnatin ta hana shi shiga Kano na tsawon akalla shekara uku.
Don haka ya ce “Shugaba Tinubu ya cika da mamaki; Ai kai ma za ka yi mamaki a ce mutum sayar da jami’a daya tilo da ake da ita, — ya rusa jami’a.
“Tsohuwar Daula Hotel da (Ganduje) ya rusa ta har kasa, tsangaya ce a karkashin Jami’ar Kimiyya da Fasaha. Wannan ba abin mamaki ba ne?
“Shi ya sa shugaban kasa ya yi, saboda da farko bai san ainihin abin da ke faruwa ba. Ya shaida min cewa ya sa a bincika masa, amma da na yi masa bayyana masa, na ce masa ‘kai Musulmi ne, kuma kwanan nan za ka je hutun Babbar Sallah, ai ba za ka so iya sallah a irin wannan wuri a cikin irin wanann yanayi ba.
“Hatta Triumph da yake magana kai dan jarida ne, kuma ya kamata abin ya ba ka haushi saboda kai ma ya shafe ka, saboda ya rusa wurin, ko’ina ya gina shaguna.
Cika alkawari ne
A cewar Kwankwaso, Gwamnan Jami’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ba wani abu yake yi ba, face cika alkawuran yakin neman zabe da ya dauka na rushe irin wadannan gine-gine.
“Don haka abin da gwamna ya yi alkawari a yakin neman zabe yake aiwatarwa.
“Ni ma ai na tsaya takarar shugaban kasa, kuma na yi yakin neman zabe, inda na yi alkawura, kuma da na je Kano sai da na shaida musu cewa irin wadannan wurare da na makarantun, wadanda yawanci aka ci filayensu, sai mun mayar musu da filayen nasu.”
Tinubu zai ba wa Kwankwaso mukamin minista
Game da yiwuwar ba shi mukamin minista a Gwamnatin Tinubu, Kwankwaso ya ce ana kan tattunawa a kan hakan, amma dai bai yi karin haske ba, game da inda aka kwana.
Sai dai kuma ya karyata masu cewa zai komawa jam’iyyar APC mai mulki, inda ya ce abin da Shugaba Tinubu ya fi damuwa a samu shi ne gwamnatin hadin kan kasa.
Ya kwatanta Ganduje da holoko, wanda ya dauka a matsayin mashawarci na musamman, kafin dagaba baya ya daga likafarsa zuwa matsayin mataimakinsa a lokacin da yake gwamnan Kano.