✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da mun hadu da Kwankwaso da na dalla masa mari — Ganduje

Na ji takaicin ganawar da Kwankwaso ya yi da Tinubu.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce da sun hadu da  takwaransa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a Fadar Shugaban Kasa da ya dalla masa mari.

Dokta Ganduje ya bayyana haka ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja da yammacin Juma’a bayan ya kai wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu karar Gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf.

Ya ce ya je fadar shugaban Kasa ne kai karar Gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf kan yadda yake rushe gine-gine a wuraren da shi Gandujen ya bayar a zamanin mulkinsa.

Yana cikin Villa ne kuma Sanata Rabi’u Kwankwaso suka shiga wata tattaunawar sirri da Shugaban Kasa Bola Tinubu, lamarin da ya sa Dokta Ganduje ya bayyana takaicinsa da zuwan Sanata Kwankwason.

“Ba mu hadu da shi ba, amma da na gan shi da zan iya kantsa masa mari saboda barnar da ya kawo a Kano,” in ji Ganduje.