✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da Kwankwaso ya ce kan nasarar Obaseki a zaben Edo

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya taya Gwamna Godwin Obaseki da al’ummar Jihar Edo murnar sake cin zaben gwamnan jihar da aka…

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya taya Gwamna Godwin Obaseki da al’ummar Jihar Edo murnar sake cin zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar.

Kwankwaso, a sakonsa na ranar Litinin ya ce gargadin da Amurka da Ingila suka yi na daukar mataki a kan masu magudi da haddasa rikici a lokutan zabe ya yi tasiri matuka.

Ya ce, “Ina godiya ga wakilan kasashen duniya da ke Najeriya musamman Ofishin Jakadancin Amurka da na Ingila da ke Najeriya game da gargadin da suka fitar dangane da masu magudi da tayar da tarzoma a lokacin zabe.

“Hakan ya yi kyakkyawan tasiri wajen razana masu magudi da tayar da rikici a lokutan zabe saboda sun san cewa akwai sakamakon da zai biyo baya.

“Mun gode da sha’awarar da kuka nuna ta zurfafa dimokuradiyya a kasarmu”, inji sanarwar.

Sanarwar da Sakatarensa Muhammad Inuwa Ali ya fitar, ta ce nasarar da mutanen Edo suka tabbatar a zaben gwamnan ya kara nuna hakikanin tasirin dimokuradiyya a Najeriya.