‘Yan Majalisar Tarayya na gudun a bayyana wa ‘yan Najeriya yawan albashi da alawus-alawus din da ake biyan su ne saboda dalilan tsaron kasa.
Sanata Micheal Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa ya sha neman a rika bayyana wa ‘yan kasa kudaden da ake biyan ‘yan majalisar amma wasu takwarorinsa ba sa goyon baya saboda abin da suka kira dalilai na tsaro.
‘Yan Najeriya sun sha yin surutai a kan yawan albashi da alawus-alawus din ‘yan Majalisar Tarayya inda wasunsu ke kira da a zaftare kudaden.
Dokokin da suka tayar da kura
Sanata Bamidele wanda ke shugabantar Kwamitin Shari’a da Hakkoki na Majalisar Dattawa, ya ce wasu kudurorin doka da ke gaban Majalisar sun sa ‘yan Najeriya yi wa Majalisar gurguwar fahimta.
Wasu kudurorin doka na kashin kai da wasu ‘yan suka gabatar a cikin shekara guda sun tayar da kura game da dacewar dokokin da kuma hadafinsu.
Daga cikinsu akwai kudirin dokar lura da kafafen sada zumunta da ta dokar hukunta masu yin kalaman tsana.
Sauran su ne dokar kafa hukumar kula da tubabbun mayakan Boko Haram da dokar hana amfani da injinan janareto da kuma ta dokar cututtuka masu yaduwa.
‘An yi mana guguwar fahimta’
Amma a zantawarsa da ‘yan jarida Sanata Bamidele ya ce ‘yan Najeriya sun yi wa kudurorin mummunar fahimta ba tare da lura da dalilan ‘yan majalisar da suka gabatar da su ba.
Ya ce, “A cikin shekara daya da ta wuce wasu kudurori sun ja mana bakin jini, duk da cewa sanatocin da suka gabatar da su sun yi ne da kyawawan manufofi.
“Sai dai yawancin mutane ba su fahimci tsarin aikin majalisa ba. Ba a dora wa majalisa laifi saboda ta yi karatun farko a kan kudirin dokar kashin kai da wani Sanata ya gabatar, komai munin kudirin.
“Muna da sanatoci 108 da za su yi nazari a kan kudirin, sannan su mahawara a kansa a lokacin karatu na biyu a kai.
“Daga nan sai a gabatar da shi domin jin ra’ayoyi da gudunmuwar jama’a. Akan yi watsi da kudurorin doka saboda rashin karbuwarsu a lokacin jin ra’ayoyin ‘yan kasa, kuma maganar ta mutu ke nan.
“Amma yawanci ana yi wa majalisar hukunci ne da kudurorin da ta yi wa karatun farko, musamman a shafukan zumunta, alhali alheri suke nufi”, inji shi.