✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Abin da ke ci gaba da haifar da karancin mai’

Mataimakin Shugaban kungiyar Dillalan Mai ta (IPMAN) Abubakar Maigandi dakingari ya ce abin da yake ci gaba da haifar da rashin wadatar man fetur a…

Mataimakin Shugaban kungiyar Dillalan Mai ta (IPMAN) Abubakar Maigandi dakingari ya ce abin da yake ci gaba da haifar da rashin wadatar man fetur a kasar nan shi ne gwamnati ba ta biya su bashin da suke bi ba tukuna.
A cewarsa “Da ake cewa gwamnati ta biya Naira biliyan 400 da miliyan 13, ba su aka biya ba, ainahin wadanda suke shigowa da mai ciki kasa su ne aka biya kudin, sun biya bashi ne ga wadanda ke shigowa da mai saboda sun biya kudin amma ba a ba mu mai ba, sun kuma biya kudi ga Kamfanin Mai na kasa NNPC, kuma shi kansa har yanzu ya kasa ba mu mai.”
Ya bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu, idan gwamnati ba ta tashi tsaye ba a ganinsa wannan matsala za ta ci gaba “Saboda sai idan akwai abu ne za a zo a sayar da shi, idan aka duba aikin da matatun suke yi bai taka kara ya karya ba. Domin kalilan ne suke iya tacewa, har yau mun dogara ne wajen shigo da kusan kashi 80 na mai, to ’yan kasuwar da ya kamata su shigo da mai, idan suka je waje su sai su gaya musu har yanzu mansu bai shigo ba, idan kuma mansu bai zo ba yana nufi ke nan ba mai,” inji shi.
Ya kara da cewa “Abin da ya sa ake ganin gidajen man NNPC kadai ke da mai shi ne, su ne ke rike da man suke ba gidajen mansu, amma ’yan kasuwan mai da ke zaman kansu ke da kashi 80, dole a samu dogon layi a gidajen mai idan har su ba su samu ba, saboda suke cikin karkara da birane.”
Daga nan ya ce suna da kudin da suke bi na dakon mai a motoci, amma har yanzu ba a samu ba. Kodayake, ya ce ba shi ne yake hana su kawo mai su raba a gidajen mansu ba,  “A’a ,rashin man da ba a samu ba ne dalili,” inji shi.
A karshe ya ce mafita idan har gwamnati za ta ci gaba da ba da wannan tallafi, sai an tabbatar cewa tallafin ana ba da shi ba tare da katsewa ba. Ya ce “Idan kuma gwamnati ta ga akwai nauyi sosai wurin yin haka yana da kyau a bar ’yan kasuwa su shigo da mai da kansu su sai su yi kamar yadda wasu kasashen duniya ke yi.”