Shugaban ’Yan Sandan Najeriya mai barin gado, Mohammed Adamu ya umarci jami’an Rundunar da su tabbata sun kamo maharan da suka kai farmaki a Hedikwatar ’Yan Sanda da Gidan Yarin a Owerrri, Jihar Imo.
Bayan ziyarar gani da ido a wuraren da aka kai harin, Adamu ya ce tabbas kungiyar IPOB mai rakadin kafa kasar Biafra ce ta kai harin tare da sakin mutum fiye da 2,000 da ke tsare.
- Dalilai uku na sauke Sufeto Janar Mohammed Adamu
- An sake kai wa ofishin ’yan sanda hari a Imo
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 8 sun sace 28 a Kaduna
- Ganduje ya zaftare albashin masu rike da mukaman siyasa a Kano
Adamu, ya ce IPOB ta kwana sanin cewa ba za taba tsere wa Rundunar ba, sannan ya umarci jami’ansa da su yi amfani da karfin makamansu a kan ’yan kungiyar.
“Za mu bi su duk inda suke da maboya, a gida ne ko a jeji, sai mun kamo su.
“Na umarci jami’anmu da su yi amfani da karfinmu na bindiga, saboda mu ke da hurumin kare kasa ba su ba. Ba za mu bari masu laifi su samu nasara ba,” inji shi.
A jawabinsa ga jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, Adamu ya ba su kwarin gwiwar cewa kar su karaya da abin da harin, su tashi su fatattaki bata-garin.
Shi ma da yake bayani, Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya ce an kai harin ne da nufin razana mutane, amma ya tabbatar wa mutanen jihar cewa gwamnatinsa na yin duk abin da za ta iya na tabbatar da ganin irin haka bai sake faruwa ba.
Tuni dai Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya ba da umarnin maye gurbin kayan da aka lalata a Gidan Yarinn Owerri da sauran abubuwan da ke barazana ga tsaron wurin.
Aregbesola ya kuma yi kira ga fursunonin da suka tsere da su dawo da kansu, in ba haka ba su shirya fuskantar sakamakon abin da suka aikata.
Ya ce wadanda suka dawo da kansu za a yi musu afuwar tserewar da suka yi, sannan ya yi alkawarin kamowa da kuma hukunta wadanda suka tsere.