✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da doka ta ce kan fanshon tsofaffin gwamnoni a Najeriya

Tun bayan da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari ya nemi Gwamnan Jihar Alhaji  Bello Matwalle  ya biya shi hakkokinsa da doka ta tanada…

Tun bayan da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari ya nemi Gwamnan Jihar Alhaji  Bello Matwalle  ya biya shi hakkokinsa da doka ta tanada da suka hada da fansho da Naira miliyan 10, don kula da kansa ’yan Najeriya ke ta ce-ce-ku-ce kan halacci ko akasinsa kan fanshon ga tsofaffin gwamnonin da wadansu zababbu.

Malam Kabir Dakata na Kungiyar CITAD ya ce kididdigar da suka yi ta nuna “Za a iya amfani da Naira miliyan 10 wajen biyan ma’aikata 333 albashi mafi kankanta na wata daya a Jihar Zamfara,” inji shi.

Wani bincike da gidan rediyon BBC ya gudanar ya nuna cewa fiye da jihohin Najeriya 20 ne suke da dokar fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansu da shugabannin majalisu.

Sai dai kudaden fanshon jihohin Zamfara da Kaduna ne suka fito fili a baya-bayan nan, inda a Jihar Zamfara ake bai wa tsofaffin gwamnonin Naira miliyan 10 duk wata.

Ita kuwa Jihar Kaduna, kamar yadda tsohon Gwamnan Jihar, Malam Balarabe Musa ya shaida wa BBC, yana karbar Naira dubu  741 ne  duk wata a matsayin fansho.

Har wa yau, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa Naira dubu 667, yake karba.

Alhaji Sule Lamido ya fadi haka ne a  martanin da ya mayar ga labarin fanshon su Balarabe Musa da BBC ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Binciken da BBC ya yi bai gano hakikanin yawan kudin da tsoffin gwamnoni ke karba ba a Jihar Kano kasancewar abubuwa ne da dama a cikin kunshin fanshon nasu kamar haka:

Gida mai daki shida ga Gwamna, inda mataimakinsa kuma zai samu gida mai daki hudu

Ofis mai dauke da kayan aiki

Albashi kamar na Gwamna mai ci

Samun kula da lafiya

Hutun kwana 30 a duk kasar da yake so

Direbobi guda biyu ga Gwamna

Mene ne fansho?

Fansho na nufin wani tanadi da ake yi wa ma’aikaci lokacin da yake bakin aiki domin cin gajiya bayan barin aiki da manufar kange shi daga taba dukiyar dukiyar.

Kwamared Kabiru Dakata ya ce dokar fansho ta Najeriya ta 2004 wadda aka yi wa gyaran fuska a 2014 ta tanadi cewa:

Ma’aikaci zai bayar da akalla kashi 10 na albashinsa

gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu za su bayar da akalla kashi takwas kan abin da ma’aikacinsu ya biya.

Sai dai dokar ta kara da cewa akwai damar sake yin waiwaye ga yawan kudin ma’aikatan lokaci zuwa lokaci.

Tsoffin shugabanni da dokar fanshon Najeriya

Dokar fansho ta Najeriya dai ba ta yi wani tanadi na musamman ba ga wani mai rike da mukami lokacin da zai bar kujera.

Sai dai hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya (RMAFC) ta yi tanadi ga masu rike da kujerun siyasa a lokacin barin ofis.

Hukumar ta tanadi cewa za a ba su kashi 300 na gwargwadon albashinsu na shekara guda a matsayin sallama.

Tanade-tanaden na RMAFC sun kuma ce tsoffin gwamnoni na da abubuwa kamar haka:

Sababbin motoci da za a rika sauyawa a duk tsawon shekara uku ko hudu.

Gina musu gida a babban birnin jiha ko kuma birnin Abuja.

Biya musu yin hutu na kwana 30 a kasar waje da kula da lafiyarsu da iyalansu.

Wannan na nufin ke nan dokar fansho ta tsoffin shugabanni a jihohi ta yi karo da dokar fansho ta Najeriya wadda aka yi wa kwaskwarima a 2014 da kuma tanade-tanaden Hukumar RMAFC.

Malam Kabir Dakata na CITAD ya ce lokacin da jihohi suka fara aiwatar da dokar fansho sun fara a kan gwamnoni ne kawai, daga bisani suka shigar da mataimakansu da shugabannin majalisa.

Kabir Dakata ya ce “Idan aka yi wasa to za a kai lokacin da za a yanka wa kwamishinoni da sauran ’yan majalisa fansho.

“Al’amarin da zai janyo kashe makudan kudi ga tsirarun ’yan kasa,” inji shi.

Shugaban Kungiyar CISLAC mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Awwal Rafsanjani ya yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle kan soke dokar bai wa tsofaffin shugabannin fansho.

Rafsanjani ya bukaci gwamnatin Shugaba Buhari da sauran na jihohi su yi koyi da Gwamnan Jihar Zamfara.

Masu rajin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na ganin idan ba a yi wa tufkar hanci a yanzu ba, to za a kai ga lokacin da kaso mai tsoka na kasafin manyan ayyuka zai kasa samuwa.

Kabiru Dakata na ganin lokaci ya yi da ya kamata a yi koyi da Gwamnatin Jihar Zamfara wajen soke fansho ga tsofaffin gwamnonin. “Idan aka yi dubi kan makudan kudin da suke karba ta hanyoyi da dama da suka hada da kudaden tsaro, za mu fahimci ba su makudan kudin fansho bai kamata ba,” inji shi.

An samu irin wannan ce-ce-ku-ce a 2017 lokacin da Najeriya ta fada haliin karyewar tattalin arziki, a wata biyu kasar ta kashe wa tsofaffin gwamnonin jihohi 21 fiye da Naira bilyan 40 da sunan fansho.

A baya-bayan nan ne dai Shugaba Buhari ya sanar da tsuke bakin aljihun gwamnati, al’amarin da ya sa Shugaban ya rage yawan ma’aikata masu taimaka wa Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Abin jira a gani shi ne ko gwamnati za ta amsa kiraye-kirayen ’yan Najeriya wajen daukar matakin kan fanshon tsofaffin gwamnonin da mataimakansu.