✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abdullahi Abbas zai maka Dederi a kotu kan zargin APC da murɗe shari’ar Gwamnan Kano

Shugaban jam'iyyar APC a jihar ya ce ya shiga tsaka mai wuya bayan kalaman da Dederi ya yi.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bai wa Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’ar jihar, Haruna Isa Dederi wa’adin awa 48 ya janye kalaman zargin bayar da cin hanci da shugabannin APC suka yi dangane da shari’ar zaben gwamnan jihar.

Wannan barazana ta daukar matakin shari’a na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 23 ga watan Nuwamban 2023, wadda ya aike wa Dederi, kuma aka raba wa manema labarai ranar Lahadi a Abuja.

Abbas ya ce Kwamishina Dederi ya zargi shugabannin jam’iyyar APC da yin uwa da makarbiya a hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano da kuma Alkalan Kotun suka yanke na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP daga kujerarsa.

Ya ce Dederi ya zargi shugabannin jam’iyyar APC da “katsa-ladan kan hukuncin da kotun ta yanke ta daga nesa ta manhajar Zoom.”

Wasikar ta kara da cewa, “Tun bayan kalamansa na fara samun kiran waya da sakonni daga ‘yan uwa da abokan arziki suna neman ba’asi a kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

“An yi min barazana da yunkurin kai hari gidana da ke Kano. Kalamanku na haifar da tashin hankali sosai, suna zubar min da mutunci a cikin al’umma.”

Amma da yake mayar da martani, Dederi, a zantawarsa da Aminiya, ya ce bai samu wata wasika daga shugaban jam’iyyar APCn ba.

Ya kara da cewa “Ban sani ba, zage-zage ne kawai. Kuma wasu sun fada min cewa sun gani a shafukan sada zumunta amma ba ni da abin cewa.

“Idan za a iya bayyana min inda na fadi hakan da abin da na fada, zan iya amsawa ko yin karin haske,” in ji Dederi.

A halin yanzu dai ana ci gaba da dakon hukuncin da Kotun Koli za ta yanke dangane da tankiyar da ta dabaibaye shari’ar Zaben Gwamnan Kano.

Ana iya tuna cewa, Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da kuma Kotun Daukaka Kara a hukuncin da suka zartar, sun ce dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ne ya lashe zaben Gwamnan Kano, sabanin Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta tabbatar.