✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya nemi Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin Hajjin 2025

Gwamnan ya jinjina wa Ƙasar Saudiyya bisa dawo wa alhazan kuɗaɗensu.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta rage kuɗin Aikin Hajjin 2025, saboda matsin tattalin arziƙin da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Gwamnan, ya yi wannan kiran ne yayin taron da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, ta shirya don mayar wa alhazan da suka yi aikin Hajjin 2023 Naira miliyan 375.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa an mayar da kuɗin ne saboda matsalar wutar lantarki da aka fuskanta yayin gudanar da Hajjin 2023.

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbaffa, ya sanar da cewa an karɓi Naira miliyan 375 daga mahukuntan Saudiyya kuma an raba wa alhazan da abin ya shafa.

Gwamnan ya gode wa Gwamnatin Saudiyya saboda ɗaukar mataki cikin gaggawa tare da dawo da kuɗaɗen.

Har ila yau, ya yaba wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kasa (NAHCON), kan yadda ta dawo da kuɗaɗen mayar cikin tsari.

Ya jinjina wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano, bisa nasarar shirya Hajjin 2023.

Sannan ya buƙaci hukumar da ta ci gaba da nuna ƙwarewa a shirye-shiryen aikin Hajjin bana.