Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike da sunayen wasu mutum shida ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewa da su a matsayin sabbin kwamishinoni a ma’aikatun gwamnati daban-daban.
Wannan ya biyo bayan sauye-sauyen da ya yi a majalisar zartarwar gwamnatin, wanda ya haɗa da soke muƙamin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar.
- Miji ya ƙona kansa da matarsa a cikin ɗaki
- NAJERIYA A YAU: Rayuwar Maza Masu Fama Da Matsalar Rashin Haihuwa
Har ila yau, gwamnan ya sallami Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Bichi, da kuma sauke wasu kwamishinoni biyar.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Isma’il Jibrin Falgore, ne ya sanar da sunayen waɗanda gwamnan ya aike a zaman majalisar da aka yi ranar Litinin.
Daga cikin waɗanda aka zaɓa akwai Shehu Sagagi, Dokta Dahiru Mohd Hashim, Ibrahim Abdullahi Wayya, Dokta Isma’il Dan Maraya, Gaddafi Sani Shehu, da Abdulkadir AbdulSalam.
Shehu Sagagi, wanda aka sauke daga muƙamin Shugaban Ma’aikata, an sake naɗa shi a matsayin Sakataren Kwamitin Shura.
Haka kuma, Ibrahim Abdullahi Wayya, ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa, shi ne tsohon Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Jama’ar Kano (KCSF).
Amma an sha zargar Wayya da nuna ɓangaranci da da ƙin goyon bayan gwamnatin NNPP.
A ɗaya bangaren, Dokta Dahiru Mohd Hashim, shi ne Shugaban Shirin Resilient Kano Agro-Climatic Project (ACReSAL).
Bankin Duniya ne ke ɗaukar nauyi don magance matsalar sauyin yanayi da lalacewar filaye a jihohin Arewacin Najeriya guda 19 da Babban Birnin Tarayya.