Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa wa Sarkin Gaya da aka sake naɗawa, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, sandar mulki.
A yanzu, sarkin na da matsayi na sarki mai daraja ta biyu.
Aminiya ta ruwaito cewa an dawo da Sarki Abdulkadir ne bayan sake naɗa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Sarki Abdulkadir ya amince da sauke shi da Gwamnatin Kano ta yi bayan soke dokar masarautun jihar da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta yi, amma daga baya gwamnan ya sake naɗa shi.
A yayin miƙa sandar mulkin, Gwamna Abba ya buƙaci sarkin da ya zama abin koyi kuma ya jagoranci mutanensa yadda ya kamata.
Gwamnan ya yaba da halin gaskiya da riƙon amana da sauƙin kai na sarkin, sannan ya gargaɗe shi da ya zauna lafiya da al’ummarsa.
Ya kuma bayyana rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’ummarsu.
Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya gaji mahaifinsa, Ibrahim Abdulkadir, wanda ya rasu a ranar 22 ga watan Satumba 2023, yana da shekara 91.
Kafin naɗinsa, Abdulkadir yana riƙe da sarautar Ciroman Gaya.
Taron na miƙa sandar ya samu halartar sarakunan Kano, Rano, Karaye, da sauran manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya.