Tun bayan da aka tabbatar da cewa Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari, hankalin wasu jami’an gwamnati manya da kanana ya tashi.
Tuni dai wasu daga cikin jami’an suka shiga daukar matakai iri-iri: misali, yayin da Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya killace kansa, takwaran aikinsa na Jihar Bayelsa, musanta zargin cewa ya yi mu’amala da Malam Abba Kyari ya yi.
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ta cikin wani sako da mai magana da yawunsa, Laolu Akande, ya aike wa wakilin Daily Trust a Fadar Shugaban Kasa, ya ce an yi masa gwaji, kuma sakamakon ya nuna ba ya dauke da cutar.
Bayan haka, Mista Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Farfesa Osinbajo “ya ci gaba da aiki daga ofishinsa dake gida kuma a halin yanzu ya killace kansa kamar yadda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduawa (NCDC) ta ba da shawara”.
Idan muka koma Jihar Ekiti, a wata sanarwa ta hannun sakatarensa na yada labarai Yinka Oyebode, Mista Fayemi, wanda ya halarci taron gwamnonin APC a Abuja ranar 16 ga watan Maris, taron da Malam abba Kyari ma ya halarta, ya ce tuni ya dauki matakin ganin cutar ba ta yadu a jiharsa ba.
“Ba wani abin daga hankali a nan. Na dauki wannan mataki ne kawai don yin riga-kafi…”
Ya kuma kara da cewa ya yi mu’amala da “wadanda ake zargin suna dauke da cutar, don haka na ga dacewar daukar wannan mataki don taimakawa a shawo kan lamarin”.
Shi ma Gwamna Godwin Obaseki, wanda suka halarci taron gwamnonin na APC tare da Malam Abba Kyari, ya killace kansa. Amma hakan bai hana shi ci gaba da aiki ba, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A cewarsa, “Bikin magaji ba ya hana na magajiya… Na shagaltu da aiki yayin da nake jiran sakamakon gwajin da aka yi min na COVID-19 bayan na killace kaina”.
Hadarin da gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja ke fuskanta ka iya futowa daga daya ko ma duka daga cikin hanyoyi biyu.
Bayan ya halarci taron gwamnonin APC ya kuma halarci taron Kungiyar Gwamnonin Najeriya, inda suka hadu da Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi, wanda shi ma aka tabbatar yana dauke da cutar.
Wata sanarwa da sakatariyarsa ta yada labarai Mary Noel Berje ta fitar ta ce shi ma ya killace kansa.
“Ganin cewa a tsawon makon da ya gabata na kasance a Abuja inda na halarci taron gwamnonin APC da Shugaban Kasa, da taron Kungiyar Gwamnoni, da taron Majalisar Kasa ta Tattalin Arziki, da kuma taron Karin kumallo na Bankin Duniya, don na zama abin koyi na killace kaina ina jira a min gwaji ni da iyalina”, inji Gwamna Sani Bello.
Shi kuwa Gwamna Diri na Jihar Bayelsa, cewa ya yi bai ga dalilin killace kansa ba duk da ya halarci taron Majalisar Kasa ta Tattalin Arziki (NEC).
Gwamnan ya fadi hakan ne da yake mayar da martini ga kiran da al’ummar jihar suka yi a gare shi ya killace kansa lokacin da ya ziyarci cibiyar da aka ware don killace masu fama da cutar a birnin Yenagoa.
“A lokacin da aka yi taron NEC Abba Kyari bay a nan, an fada mana cewa ya tafi Jamus…
“Game da Bala Muhammed kuwa, gaskiya ne ko wane lokaci muna zauna kusa da juna, amma a lokacin bai kamu da cutar ba”.