✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Kyari ya ce ’yan IPOB ne suka kulla masa sharri

Kyari ya ce IPOB/ESN ne suka kulla masa sharri don bata masa suna saboda ya ragargaje su a yankin Kudu maso Gabas

Fitaccen dan sandan nan da aka tsare a baya-bayan nan kan badakalar hodar Iblis, DCP Abba Kyari, ya zargi kungiyar IPOB da ke Kudancin Najeriya da kulla masa sharri.

Abba Kyari ya ce IPOB da reshenta na ESN ne suka kulla masa sharri da nufin bata masa suna, saboda ragargazar su da ya rika yi a yankin Kudu masa Gabashin Najeriya.

Ya yi zargin ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin da Hedikwatar ’Yan Sandan Najeriya ta kafa domin binciken zargin da ake masa na saba ka’idar aiki.

Rahoton kwamitin ya ce Abba Kyari ya shaida masa cewa, “IPOB/ESN ne suka shirya makarkashiya domin bata masa suna saboda ya ragargaje su a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.”

Kwamitin wanda Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Joseph Egbunike, yake jagoranta, ya yi watsi da zargin na Abba Kyari a matsayin soki-burutsu.

Rahoton kwamitin ya kara da cewa Abba Kyari bai musanta cewa ya yi kunnen kashi ba wajen saba dokar aikin dan sanda a yadda ya rika amfani da kafofin sada zumunta, duk kuwa da cewa an sha yi masa gargadi a kan hakan.

Rahoton kwamitin dai shi ne wanda Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya mika wa Hukumar Aikin Dan Sanda, da ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi daga DCP zuwa ACP.

Idan ba a manta ba, Abba Kyari na kuma fusknatar zargin alaka da Badakalar Hushpuppi, wadda ta danganci damfara ta daruruwan miliyoyin daloli a kasashen waje.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ko Hukumar Aikin Dan Sanda ta yi watsi da rahoton da aka mika mata sun shekarar da ta gabata, kamar yadda ake rade-radi, amma abin ya faskara.

Wakilin namu ya yi ta kirar Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani, amma babu amsa, kazalika babu amsar rubutaccen sakon da wakilin namu ya tura masa.

Kazalika shi ma Mukaddashin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, bai samu amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da wakilinmu ya yi masa ba.

Wakilinmu ya nemi Adejobi ne domin samun karin haske game da zargin rufa-rufa a kan batun na Abba Kyari da kuma wa’adin mako biyu da hukumar aikin dan sanda ta ba wa runduna a kan binciken.

A ranar Laraba, Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya da manyan hafsoshin rundunar sun ziyarci Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, a ofishinsa da ke Kotun Koli a Abuja.

Wani babban hafsan dan sanda ya shaida wa wakilinmu cewa ziyarar na da alaka da batun Abba Kyari.

Amma, sanarwar da rundunar ta fitar ta bayyana cewa ta kai ziyarar ce domin kyautata alaka tsakanin ’yan sanda da bangaren shari’a a matsayin masu ruwa da tsaki wajen hukunta masu aikata manyan laifuka domin komai ya tafi daidai a Najeriya.