Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Injiniya Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin zababben Gwamnan Kano a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Da yake bayyana sakamakon zaben, Shugaban Tattara Sakamakon Zaben, Farfesa Ahmad Tukur Ibrahim, wanda malami ne a Jamiar Ahmadu Bello da ke Zariya ya bayyana cewa Abba ya yi nasara da kuri’u 1,019,602.
Wanda ya zo na biyu a zaben shi ne Nasir Yusuf Gawuna, na Jam’iyyar APC kuma mataimatin gwamna mai ci, wanda ya samu kuri’u 890,705; tazarar kuri’un da ke tsakanin ‘yan takarar 128, 897, daga ciki kuri’u 2,004,964 da aka jefa a zaben.
Karo na biyu ke nan da Abba ya tsaya takarar Gwamnan Kano, inda a 2019 ya tsaya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Sai dai a wancan karon ya sha kaye a hannun Gwamnan Abdullahi Ganduje, a zaben mai cike da rudani.
Abba ya kasance Kwamishinan Ayyyuka a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Kawo yanzu Jihar Kano cewa kadai NNPP ta lashe zaben gwamna, a yayin da INEC ke ci gaba da tattara sakamakon zaben jihohi.
Hakazalika Kano, mahaifar Kwankwaso wanda shi ne dan dan takarar shugaban kasa na NNPP, ta kasance cibiyar jam’iyyar a wannan karon, inda take da sanatoci biyu da kuma ‘yan majilar tarayya da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa kawo yanzu APC ta lashe zaben gwamnoni a jihohi takwas, a yayin da PDP ke da hudu.