✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Abba Gida-Gida ya sanya hannu kan kasafin 2024

Kashi 64 na kasafin na N437bn an ware shi ne ga manyan ayyuka, ragowar kashi 36 kuma na ayyukan yau da kullum.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan kasafin kudin jihar na shekarar 2024 na Naira biliyan 437.

Kashi 64 cikin 100 na kasafin an ware shi ne ga manyan ayyuka, ragowar kashi 36 kuma na ayyukan yau da kullum.

Gwamnan ya sanya hannu domin zaman kudurin kasafin doka ne bayan samun amincewar Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Bayan kammala aikin kwamitin ne babban zauren majalisar ya amince da kasafin da gwamnan ya gabatar mata.

Bayan kammala karatun majalisar na kan kudurin dokar ne majalisar ta gabatar da shi ga bangaren zartarwa domin gwamna Abba ta rattaba hannu.

Shugaban Masu Rinjaye na majlisar, Lawan Hussaini (NNPP-Dala), jim kadan bayan sanya hannun gwamnan ya ce kasafin zai ba da damar aiwatar da ayyukan cigaban Jihar Kano.