✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba gida-gida ya maka Ganduje a kotu

Abba Kabir Yusuf ya maka Ganduje a kotu kan zargin sayar da filin fakin

Dan takarar Gwamnan Jihar Kano karkashin jamiyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya yi karar gwamnatin jihar bisa zargin karkatar da ginin filin fakin din motoci da Gwamnatin Kwankwaso ta faro a kan titin Shahuchi kusa da Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed.

Wadanda Abba ke kara sun hada da Mudassir Abubakar da Abduusamad Sammani da Hukumar Kasa da Safiyo da Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kano da Ma’aikatar Gidaje da sufuri ta Jihar Kano da kuma Kwamishinan Sharia na Jihar Kano.

Takardar karar mai shafi 26 ta na zargin Gwamnatin Ganduje ta cefanar da ginin filin fakin din wanda na alumma ne ga wadanda ake kara na biyu da na uku don amfanin kashin kansu, lamarin da ya saba da sashe na 1 da na 51 (1) na dokar amfani da kasa.

Filin fakin din wanda gwamnatin da ta gabata ta faro aikinsa don rage cunkoson ababen hawa akan titin zuwa Asibitin na Murtala Mohammed an cimma kaso 68 na kammala aikin.

Har ila yau takardar karar ta bayyana cewa filin fakin din da ke da tsawon Mira 43,969 ko kuma kwatankwacin kadada hudu.