Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce har yanzu gwamnatinsa ba ta yanke hukunci kan makomar masarautun Kano da Ganduje ya samar ba sabanin rahotannin da ake yadawa.
Bayanin gwamnan na zuwa ne a wani martani na karyata rahoton da ake yadawa cewar zai rushe masarautun baki daya tare da dawo da Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano baki daya.
- Cire Tallafi: Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya fito da hanyoyin rage radadi
- BIDIYO: Ra’ayoyin Kanawa game da rushe shatale-shatalen kofar gidan Gwamna
An rawaito cewar za a mika wa sabuwar Majalisar Dokokin Jihar kudurin rushe masarautun a ranar Alhamis, wanda aka ce ake sa ran shugaban masu rinjaye na majalisar jihar, Lawan Hussaini zai gabatar.
Sai dai duk da karyata wannan labari da Hussaini ya yi jim kadan bayan zaman majalisar a ranar Laraba, hakan bai hana labarin zama wutar daji ba.
Gwamnan ta hannun Sanusi Bature, Sakataren Yada Labaransa a yammacin Laraba ya fitar da wata sanarwa, inda ya yi watsi da rahoton.
“Sabanin jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta, gwamnatin Jihar Kano ba ta dauki wani mataki kan sabbin masarautu ba,” in ji sanarwar.
Bature ya ce, huldar da ke tsakanin bangaren zartaswa da na majalisar dokoki a Kano za ta kasance a bayyane domin bai wa mutanen Kano damar samun bayanai kan manyan manufofi da kudirorin gwamnatin NNPP.
Ya ce wakili daya tilo da ke tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa tun lokacin da aka kaddamar da majalisa ta 10 shi ne bukatar da gwamnan ya yi na nada masu ba shi shawara na musamman guda 20 wanda majalisar dokokin jihar ta amince a zamanta na farko a ranar Laraba.
“Ana sa ran aike da jerin sunayen kwamishinonin da za su yi aiki a ministoci a mako mai zuwa don tabbatar da su,” in ji sanarwar.
Aminiya ta ruwaito cewa, batun rushe masarautun jihar na ci gaba da kamari tun bayan lashe zaben gwamna da jam’iyyar NNPP ta yi a watan Maris.
Hakan dai ya kara kamari bayan da shugaban jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wata hira, inda ya ce yana sa ran gwamnatin Abba za ta duba hurumin yadda aka samar da sabbin masarautun da kuma yiwuwar dawowa da Sanusi a matsayin Sarkin Kano.
Tun bayan darewar Abba mulki ya shiga rushe-rushen gine-ginen da aka yi su ba bisa ka’ida ba da kuma dawo da wasu kadarorin gwamnatin jihar da Ganduje ya siyar ba bisa ka’ida ba.