✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi taka-tsantsan kan jarraba maganin gwajin cutar Ebola

barkewar cutar Ebola na baya-bayan nan da kuma watsuwarta a kasashe da daman a Afirka ta Yamma ya jawo manyan kasasehn duniya sun shiga rige-rigen…

barkewar cutar Ebola na baya-bayan nan da kuma watsuwarta a kasashe da daman a Afirka ta Yamma ya jawo manyan kasasehn duniya sun shiga rige-rigen magance ta tare da nemo maganin da zai warkar da ita.
Zuwa yanzu dai babu maganin cutar, wadda a cewar masana cututtukan annoba tana iya kashe mutum cikin kwana 21. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta riga ta ayyana barkewar cutar ta bayan nan da yadda take yaduwa kamar wutar daji da cewa wata barazana ce ga lafiya a duniya da ke bukatar matakin gaggawa. Sama da mutum dubu ne cutar ta kashe tun barkewarta na bayan nan ’yan watannin da suka gabata, kuma galibin wadanda suka mutu sun fito ne daga Laberiya, wadda daga can ne wani dan kasarta Mista Patrcik Sawyer da ke fama da Ebola ya shigo wani jirgi zuwa Najeriya a watan jiya.
Mista Sawyer ya mutu kwanakin kadan da isowa Najeriya a wani asibiti a Legas. Shi ne tushen jawo harbuwa da cutar a Najeriya, inda wasu da dama suka mutu, daruruwa kuma suke karkashin sanya ido da kebewa.
Yanayi da yadda Ebola ta barke da kuma kasancewar ba ta da magani ta firgita miliyoyin jama’a. Wannan ne ya jawo aka rika yada jita-jita kan yadda za a magance ta, inda hakan ya haifar da mummunan sakamako a karshe. Tattaunawa a kafafen sadarwa na zamani cewa hada gishiri da ruwan zafi a sha na magance cutar Ebola ya yadu a Najeriya kamar wutar daji, inda ya tilasta hukumomin lafiya gaggauta tsoma baki don musanta wannan rashin kan gado. Sai dai kuma lokaci ya kure ga wasu, domin wuce kima wajen shan gishirin da mutanen suka yi ya jawo mutuwar mutane da dama a Jihar Filato da kwantar da wasu da dama a asibiti a can da wasu jihohin. Kuma yayin da jama’a ke tsakiyar fargaba da tsoro game da cutar Ebola da yadda hakan ya takaita mu’amala a tsakanin jama’a da kuma tafiye-tafiye, babu mamaki a yi haba-haba da duk wani maganin da ake jin zai magance cutar.
Amurkawan mishan biyu da suka kamu da cutar lokacin aikinsu a Afirka ta Yamma da aka mayar da su Amurka cikin tsattsauran tsaro za a yi amfani da wani maganin gwaji a kansu mai suna Zmapp da aka kirkiro a can.
Maganin wani hadi ne na wasu sinadarai uku masu kare jiki daga farmakin cutar ga abincin mai gina jiki. Rahotannin farko sun ce daya daga cikin majiyantan ya fara nuna alamun da ke karfafa gwiwa; amma ba a tabbatar da ko maganin zai iya magance Ebola ba.
Sai dai duk da haka wannan bai hana kasashen duniya neman maganin na zmapp ba. A nan Afirka, Laberiya ce kawai Amurka ta amince mata ta yi amfani da shi don jinyar masu cutar Ebola. Cutar ta bayyana a Dubai, inda wani dan Najeriya da aka yi wa jinya a kanta ya mutu. kasashe da dama sun takaita tafiye-tafiye zuwa ko daga yankunan da cutar take. Kuma karin abin bakin ciki masu yin maganin zmapp sun ce maganin ya kare. An ce Najeriya ta bukaci a ba ta maganin zmapp. Kuma a makon jiya Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta ce za a iya amfani da wani magani mai suna Nano-Silber da wani dan Najeriya da ke zaune a kasar waje ya kirkiro don maganin cutar Ebola. A nan ne ya kamata kada matsalar cutar Ebola ta sa ido ya rufe, akwai bukatar a yi taka-tsantsan wajen zabar magani a kokarin da ake yi na magance ta. Tuni aka fara samun takaddama a tsakanin jami’an Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Amurka kan da’awar ingancin maganin Nano-Silber wajen magance Ebola. Jami’an Amurka suna ganin wannan da’awa shirme ne kawai, amma Farfesa Kamiyus Gamaliel, Shugaban Kwamitin Gwamnati kan bincike da mangance cutar Ebola, ya mayar da martini cewa jami’an na “bin ka’idojin da aka shimfida kan gwajin maganin.”
Wannan muhawara tana da karfafa gwiwa, to amma yana da amfani a tuni yadda Najeriya ta samu kanta wajen gwajin magani, musamman na bayan nan abin da ya faru a Kano, wanda ya shafi kamfanin Pfizer na kasar Amurka. Baya ga mace-mace da gwajin ya haifar, lamarin nakasar daruruwa tunatarwa ce kan mugun illar da ka iya biyowa baya. Sunan Thalidomide ya kwanta a yanzu. Amma Jamusawa masu yin maganin sun zama abin suka ko’ina a mafi yawan Yammacin Turai inda ya haifar da karancin haihuwar da ke bibiyarsu tun daga shekarun 1950 zuwa 1960 kafin a haramta amfani da shi.
kalubalen da Ebola ta kawo yanzu bai kamata ya zama wata dama da wasu miyagun mutane da suke samun goyon bayan wasu jami’an gwamnati su kudance ta hanyar jefa lafiyar mutane cikin hadari ba.