A ranar Litinin din makon jiya ce 13-11-17, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shugabanci taro na musamman na Majalisar Zartarwarsa da aka gudanar a fadar shugaban kasa ta Aso Rok da ke Abuja mai taken Ilmi a Nijeriya: kalubale da abin da ake fatan ya biyo baya. A iyakacin sa ni na wannan shi ne karo na farko tunda aka fara mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, shugaban kasa ya ke jagorantar Majalisar Zartarwarsa (Majalisar da ta kunshi shugaban kasa da mataimakinsa da Ministoci), wajen yin taro irin wancan akan makomar fannin ilmin kasar nan. Abin da dai aka sa ni kuma ake yi duk shekara shi ne taron Majalisar Ilmi ta kasa da ta kunshi ministocin ilmi da dukkan kwamishinonin ilmi na jihohin kasar nan 36, taron da ya kan duba matsayin da ilmi yake ciki da inda ya dosa da kuma irin yadda za a tunkari kalubalen da yake tattare da shi da yadda za a fuskance shi don gyarawa.
A wajen bude wancan taro a jiyo shugaba Buhari yana bayyana wasu daga cikin irin abubuwan da su ka dabaibaye fannin ilmin kasar nan da suka hada da karanci da lalacewar ajujuwa da rashin kwararrun malamai da rashin kayayyakin koyo da koyarwa da kuma uwa uba kasancewar kimanin yara sama da miliyan 13, da ba sa zuwa makaranta. Shugaba Buhari ya fadi cewa ba wani boyayyen sirri ba ne a kasar nan cewa fannin ilmi yana mutakar bukatar kyakykyawar kulawa don bunkasar shi, ina mai jaddada cewa sanin kowa ne cewa fannin ilmin kasar nan yana fama da matsaloli ne bisa ga tarihin nuna halin ko in kula da rashin hangen nesa da annobar cin hanci da rashawa da suka yi katutu a kasar nan kamar yadda tarihin ya tabbatas.
Ya ci gaba da cewa ya zama wajibi kasar nan ta bayar da da kulawar da ta dace ga fannin ilmi kuma yana mai la’akari da cewa kasar nan ba za ta iya samun wani ci gaba da ya wuce matsayin ilminta. “ Dole mu samu daidai a kasar nan. Samun daidanmu, yana nufin mu sanya fannin ilminmu a kan turbar daidai,” in ji Shugaba Buhari a wajen wancan taro na musamman. Shugaba Buhari lallai ‘yan kasa su san da sanin cewa matakan tsaro da dorewar zaman lafiyar kasar nan sun dogara ne kacokan akan samar da ingantaccen ilmi a kasar nan.
Shi ma Ministan ilmi Malam Adamu Adamu a cikin nasa jawabin kira ya yi da a bayyana dokar ta baci a kan fannin na ilmi bisa ga irin yadda ya tabarbare, tare da neman lallai a kara yawan kason da ake ware wa fannin a cikin kasafin kudin kasar nan. Yana mai nuni da cewa Gwamnatin Shugaba Buhari tana bukatar Naira Tiriliyan 1, duk shekara har zuwa nan da shekaru hudu masu zuwa, abin da ya ce samuwar haka ne kawai gwamnatin za ta iya cikasa kudurori 13, da ta dauki alkawarin cikasu a fannin ilmi.
Ministan ilmin ya kuma koka da bayyana takaicinsa akan tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya a kasar nan a shekarar 1999, kason da ake warewa fannin ilmi yak an kama ne daga kashi 4 zuwa kashi 10, cikin 100, duk shekara, ya na mai cewa ba kasar da ke cikin kasashen nan na E9 da na D8, da kasar nan ta ke cikin kungiyoyinsu da suke ware wa fannin ilmi kasa da kaso 20, cikin 100, na kasafin kudinsu duk shekara sai kasar nan. Ya ce haka labarin ya ke a kasashen nahiyar Afirka, wadanda kasar nan ta fi wadata, amma duk sun fi ta zuba kudade a harkar ilmi.
Malam Adamu Adamu ya fadi cewa yanzu ne ya kamata gwamnati ta fara kara kasafin kudin fannin ilmi, kasancewar wannan gwamnatin tana da kyakykyawar aniya na kudiri na siyasa da za ta iya wannan gyara kamar yadda ta yi aniya. karin kudi kawai ake bukata don cimma wannan gagarumin aiki. Ya yi fatan za a rinka ba da tallafi kai tsaye ba da wata hiyana ba ga dukkan wadanda suke son su karanta fannin ilmin koyarwa da kuma sama mausu ayyuka kai tsaye ba tare da wata wahala ba da zarar sun kammala karatunsu. Ya yi fatan ganin ana ba da alawus-alawus ga kwararrun malamai.
Ba ko shakka a yi batun ceto fannin ilmi kuma daga koli irin na Majalisar Zartarwa ta kasa karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, wani abin a yaba ne kuma da yin maraba da kuma fatan ganin yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu. Amma kuma kar mai karatu ya manta a zaman da ake ciki na mulkin dimokuradiyya kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadi sa hannun gwamnatoci 3 a cikin tafiyar da fannin ilmi a kasar nan, baya ga irin gudunmuwar da masu makarantu masu zaman kansu da kungiyoyin iyayen yara da malamai da na tsofaffin dalibai da na kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da wajen kasar nan da sauran daidaikun ‘yan kasa, musamman masu hannu da shuni akan yadda za a iya ciyar da fannin ilmi nan gaba.
Alal misali, tsarin mulkin ya tanadi tafiyar da makarantun Firamare cikin hadin gwiwar gwamnatin jiha da Majalisar karamar Hukumar, yayin da majalisun kananan hukumomi su ke da alhakin dauka da karin girma da biyan albashin malaman makarantun Firamare da samar da kujerun zama da kayayyakin koyo da koyarwa, wani lokaci ma har da ginawa da gyaran ajujuwa, yayin da da gwamnatocin jihohi ka iya shigowa wajen tallafa wa wadannan aikace-aikace da makamantansu. Gwamnatocin jihohin suke da alhakin tafiyar da fannin ilmin gaba da Firamare, wato makarantun Sakandire da ma sauran makarantun gaba da Sakandire irin su Jami’o’i da manyan Kwalejojin ilmi da na kimiyya da fasaha da makamantan su ta fannin dauka da biyan albashin malamansu da gine-gine da gyaransu da samar da kayayyakin koyo da koyarwa su da sauran dawainiyar yau da kullum. Wadannan fannin ilmi guda biyu wato na makarantun Firamare da Sakandire su ne tushen ilmi, musamman ilmin Firamare wanda daga kansa ake barin bida baya.
Da wannan ke nan ka ga mai karatu wannan babban aiki da kalubalen da ke tattare da shi yana matukar bukatar sadaukarwar gwamnonin jihohi da shugabannin majalisun kananan hukumomi. Gwamnonin jihohi lallai su tabbatar da cewa su na da majalisun kananan hukumomin cikakkun kudin shigarsu daga asusun gwamnatin tarayya, wato dai cikakken ‘yancin cin gashin kai, su kuma shugabannin kananan majalisun hukumomi lallai su tabbatar da cewa su na tusarrafi da kudin da kuma nasu na cikin gida wajen kyautata wannan fannin da ma sauran fannonin kyautata jin dadin rayuwar al’ummarsu. Irin wannan sadaukarwa da jagoranci nagari abin misali ya kamata gwamnonin jihohi su nuna cikin tafiyar da fannin ilmi a jihohinsu.
Masu makarantu masu zaman kansu, wadanda wurin su duk wani da ya damu dansa ya samu ingantancen ilmi ya ke kai dansa ya kamata su ma su duba ta irin yadda za su rage irin yawan kudin da suke caja, da kuma ingantuwar ilmin da suke ba yara, kasancewar yanzu da makarantu masu kan nasu da na gwamnatoci duk kanwar ja ce wajen magudin jarrabawa.
A nan na ke ganin kungiyoyin malamai da iyayen yara da na tsofaffin dalibai da na kungiyoyin cikin gida da waje, duk suna da gagarumar rawar da za su taka wajen ganin ingantuwar ilmin. Yanzu kuma shi ne lokacin da za a fara fatan Allah Ya kama.