✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Yi Hattara da Bara-Gurbi

A tsakiyar watan jiya ne Shugaba Muhammadsu Buhari ya amince zai yar da kwallon magwaro don ya huta da kuda, watau ya kawo karshen guna-gunin…

A tsakiyar watan jiya ne Shugaba Muhammadsu Buhari ya amince zai yar da kwallon magwaro don ya huta da kuda, watau ya kawo karshen guna-gunin da wasu jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyarsa mai mulki ta APC ke yi game da rashin ciccike guraban mukaman da aka bar wasu ‘yan adawa da yawa bisansu, suna ta cin karensu ba babbaka, shekaru kusan uku bayan kafuwar gwamnatin da suka taru suka cicciba. A yanzu Shugaba Buhari ya ce ba ma nannada wasu zaratan ‘ya’yan jam’iyyar zai yi bisa wa]ancan mukaman ba, har ma dara yawan ministocinsa zai yi domin kuwa ya fahimci cewa a yanzu akwai matukar bukatar fadada Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Da farko dai Shugaba Buhari ya ce ba zai nannad ministoci da yawa ba  saboda yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki, amma zai zazzabo daidai daga kowace jiha don bin ka’idar da ke kunshe cikin kundin tsarin mulki da  ya bukaci  akalla kowace jiha ta samu minista. Shi ya sa da ya tashi zubin ministocin sai ya buge da cike gurabun guda talatin da shida maimakon guda arba’in da biyu da gwamnatin jam’iyyar PDP ta bar masa.  Wannan ne ya sa shi rage yawan ma’aikatun da ya gada  ta hanyar ha]e wasunsu  wuri guda. Daga cikin  ministocin da ya nada  akwai guda goma sha hudu a matsayin kananan ministoci da kuma manyan ministoci guda ashirin da biyu, ciki har da shi kansa.

To yanzu  Shugaba Buhari ya ce tun da yake tattalin arzikin kasa ya ingantu za a koma bisa waccan tafarkin ta ministoci arba’in da biyu, watau za a yi karin wasu  guda shida ke nan. An fahimci cewa Shugaba Buhari na da nufin tsattsaga wasu manyan ma’aikatun da ake da su a halin yanzu, kaman  ma’aikatar Wutar Lantarki da Ayyuka da Gidaje, ta yadda ko wanne bangare daga cikinta zai yi zaman kansa. Haka nan kuma za a raba ma’aikatar sufuri gida biyu, a samu ta sufurin jiragen kasa da kuma ta jiragen sama. Ita ma ma’aikatar aikin gona, daya daga cikin mnyan ma’aikatun da ake da su, za a raba ta biyu don a fitar da Ma’aikatar Noman Rani Da Ban Ruwa.

Kaman yadda ake rade-radi, za a kuma yi garambawul a Majalisar Zartarwa ta Ministoci, inda ake cewa za a zazzare wasu guda takwas wadanda za a maye gurabansu da wasu sabbin jini don a ji dadin gungura gwamnatin yadda ya kamata. Haka nan kuma sauran tsoffin ministocin, da ba a tankade ko aka rairaye ba, za  a cancanja masu ma’aikatun da za su dudduba. Wannan al’amari ne da ya kamata a ce an yi tun a shekarar da ta gabata, yayin da talakawa suka fara kosawa da gwamnatin, ganin yadda take jan-kafa da kuma yadda  al’amuranta ba su gudana yadda ya kamata. An ce cikin ‘yan kwanakin nan ne za a gabatar wa Majalisar Dattijai  sunayen wadanda aka zazzaba don tantancewa.

To, sa’ilin da talakawa ke murna cewa an dauki matakan zaburar da gwamnati don yin ayyukan da za su fitar da jama’a daga }angin fatara da talauci, ko kuma a ce halin kunci da matsi, sai ga shi nan kuma murnarsu na so ta koma ciki, domin kuwa Shugaba Buhari ya  dandana wannan muhimmin batu ga jam’iyyarsa da kuma gwamnonin jihohi wadanda yake gani su ne za su zazzabo masa wadanda suka fi dacewa ya tafi tare da su. Talakawa na ganin cewa da sake, ko kuma akwai gyara game da haka, domin kuwa  jam’iyyar APC dai a halin yanzu tana fama da matsaloli masu yawan gaske wadanda suka kusan kai ta kasa, saboda haka nan idan har tana cikin masu zakulo wadanda Shugaba Buhari zai nannada ministoci , to kunshi za a yi a baraka, watau za a yi ne ba a yi ba, domin zaben tumun dare kawai za a yi. Dalili kuwa shi ne  ganin  cewa bakin shugabannin jam’iyyar daya ne da na gwamnonin da ba su tare da sauran ‘ya’yan jam’iyya.

Haka nan kuma gwamnonin jihohin da  aka dan ka wa wannan amanar  ba za su yi adalci ba domin kuwa zaben tumun dare za su yi, za su mimmika sunayen ‘yan korensu ne kawai, ba za su bayar da na wadanda ke adawa da su ba saboda kauce hanya da rashin bin manofi da ka’idojin jam’iyya. Saboda haka nan maimakon daure kashi igiya kawai za a bata, kuma hakan ba zai taimaka  wajen dinke barakar da ta gauraye jihohi kusan goma sha shida da jam’iyyar APC ke mulki ba. Kawo karshen rashin  fahimtar juna da kokarin  hada kan ‘ya’yan jam’iyya ne dai makasudin yin canje-canje da nade-naden sababbin ministocin, to  sanya gwamnoni cikin al’amarin ba shi da wata fa’ida, hakan  zai }ara dagula al’amura ne.

To, amma ana iya cewa Shugaba Buhari ya nemi gwamnoni da uwar am’iyya ne su taimaka masa dangane da haka don ya kore ya sha da karari idan aka zo babban taron jam’iyyar na kasa baki daya wanda a lokacin ne za a fitar da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar, inda yake sa ran cewa gwamnoni da shugabannin jam’iyyar za su ramawa kura aniyarta, za su saka  masa da kuri’un wadanda ake kira delegates daga jihohinsu. To koma dai mene ne dalilin Shugaba Buhari na amincewa da gwamnoni da kuma uwar jam’iyya game da haka ana iya cewa wanda ya sanya takalmi shi ya fi sanin inda ya matse shi. 

Ya kamata fa a tuna cewa  mutanen da gwamnonin nan za su zazzakulo, su turawa Shugaba Buhari, suna iya kasancewa ba su ne wadanda  jama’an jihohinsu ke bukata ba, kuma wajibi ne a yi la’akari da cewa yawancin gwamnonin nan ba su danyen ganye  da ‘yan Majalisar Dattijai daga jihohinsu wa]anda kuma ta kansu za a bi kafin a tantance sabbin ministocin da za a nannada. Ashe ke nan ya wajaba a yi taka-tsantsan game da haka, ganin cewa har yanzu ana takun saka tsakanin Majalisar Dattijai da kuma bangren gwamnati, kuma batun tantance sabbin ministocin kan iya janyo sabon jidali a tsakaninsu, domin dattijan za su nuna amincewa ko akasin haka ga wadanda aka zazzabo daga jihohinsu, tun da dai  mafiya rinjaye daga cikinsu  ‘ya’yan jam’iyyar APC ne.

A karon farko dai an ce Shugaba Buhari da kansa ne ya zazzabo ministocin da ya yake aiki da su a yanzu, kuma tun kafin a tafi ko ina  sai aka fara kuka da su saboda abin da ake cewa rashin sanin makaman aiki, domin da yawansu ba ‘yan siyasa ba ne.  To, a wannan karon ya kamata Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa wadanda za a kawo masa ya yi aiki da su kwararru ne kuma  zakakuran hazikan da suka yi fice a harkokin siyasa da mulki, ba bara-gurbin  da gwamnoni za su turo masa  daga jihohi ba, waddanda  cikin dankankanen lokaci za su farfashe, su cika wuri da doyi.