Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana ya roki Shugaban Kasa Muhamamdu Bubari ya yi afuwa ga soja 70 aka yanke wa hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari saboda yin bore a wurin yaki da Boko Haram.
Falana ya yi rokon ne a cikin wata wasika, yana kira ga Shugaba Buhari ya yi amfani da matsayinsa ya sassauta hukuncin daurin shekara 10 da aka yanke wa sojojin kamar yadda ya yi wa takwarorinsu 3,002 da suka aikata irin laifin.
Ya ce ragowar sojojin su 70 da kotun soji ta yanke wa hukuncin sun cancanci samun yafiya daga Shugaban Kasa kamar yadda doka ta ba shi iko a karkashin sashe na 179 na kundin tsarin mulki.
Sojojin da hukuncin ya shafa sun yi bore ne a shekarar 2013 da 2014 kan rashin isassun kayan yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Daga baya, Falana ya sa baki aka yafe wa mutum 3,002, aka kuma dawo da su bakin aikinsu, in banda 70 suka rage a gidajen yarin Kirikiri da na Ikoyi.
Babban lauyan ya ce a zahirin gaskiya, ba bore sojojin suka yi ba, sun yi kokarin jan hankali ne kan karancin kayan yaki da Boko Haram.
Ya kara da cewa daga baya binciken kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan sayo makamai a 2015 ya gano cewa an karkatar da kimanin Dala biliyan 2.1 na sayen makaman.