✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yayin da aka yi wa jam’iyyar APC rijista

Shi ke nan, duk wata hauma-hauma, duk wani cece-kuce sun kawo karshe, domin kuwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta tabbatar da cewa ta yi…

Shi ke nan, duk wata hauma-hauma, duk wani cece-kuce sun kawo karshe, domin kuwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta tabbatar da cewa ta yi wa jam’iyyar APC rijista. Wannan kuwa ya sanya al’umma da dama sun bayyana sha’awarsu da haka. Wasu da dama suna ganin cewa yi wa jam’iyyar rijista wani al’amari ne na ci gaba mai muhimmanci a siyasar kasar nan.
A can baya, an dade ana tafiya da jam’iyya fallan-daya, inda babu wata kakkarfar jam’iyyar adawa. A kowane lokacin zabe, PDP ce babbar giwar da kan yi uwa da makarbiya, inda take da tabbacin cinye kowane zabe da aka shirya a kasar nan. A yayin da aka yi wa APC rijista, an samu kafa kakkarfar kafar adawa, kuma haka din abu ne mai amfani ga siyasar kasar nan. Abu ne mai amfani ga ita kanta PDP, domin kuwa hakan zai sanya ta jajirce, ta sake lale, yadda za ta gabatar da manufa mai kyau kuma wacce za ta gamsar da ’yan kasa. Haka kuma, wannan zai ba ’yan takara dama, su samu zabin jam’iyyar da za su iya gwada kwanjinsu, ba tare da tsoron komai ba. Wannan zai sanya jam’iyyun su rika tsayar da ’yan takara nagartattu, wadanda za su iya samun nasara, ba kawai abin da ake yi a baya ba na dauki-dora. Don haka, wannan rijista da aka yi wa APC, yana ishara ne da cewa a zaben 2015, za a samu takara da ’yan takara masu armashi, wadanda za su iya canja alkiblar mulki da siyasa a kasar nan.
A wannan gaba, ya dace a yaba wa dukkan mukarraban da suka jajirce suka bi kadin ganin an yi wa jam’iyyar rijista. Kafin a kai ga wannan nasara, mutane da dama sun rika yin dari-dari da gamayyar jam’iyyun da suka hada kai suka kafa APC, inda aka rika yin shakkun cewa al’amarin ba zai dore ba. An yi wannan hasashe ne saboda sanin tarihin kawancen jam’iyyun siyasa a can baya da kuma ganin cewa da dama daga cikin shugabannin jam’iyyun da suka yi wannan hada-ka, jiga-jigai ne a siyasar kasar nan; wanda ake ganin da kyar za su iya hakurin shan inuwa daya a siyasa. Haka kuma, an yi zargin cewa makircin PDP na iya dakile nasarar yi wa APC rijista. Tun da dai yanzu an samu rijista, to kamata ya yi kananan jam’iyyun nan da suka cika mana wuri, su fara daidaita sahunsu, su samu inda za su rakuba su taka rawa mai kyau a dimokradiyyance.
Ga shugabannin jam’iyyar kuwa, kada su dauka shi ke nan sun gama cin ma komai, don kawai Hukumar Zabe ta yi masu rijista. Akwai kalubale da jan aiki mai yawa a gaba da ya kamata su mayar da hankali. Kamata ya yi su fara aikin tattara magoya baya daga al’ummar kasa, wadanda za su kaunaci jam’iyyar kuma su ba ta goyon bayan da ya kamace ta, kada su tsaya kawai ga tsofaffin membobin jam’iyyun da suka yi hada-ka da su tun asali. Haka kuma, kada batun kururutawar da jam’iyyar ke samu daga kafafen watsa labarai ta rude su, kuma kada su dogara da cewa ai al’umma sun gaji da PDP, su dauka cewa wannan kawai za ta ba su nasara a fagen zabe. A’a, aikin ya wuce nan, ya zama wajibi su tashi tsaye domin fuskantar babban kalubale. Misali, ya dace jam’iyyar ta tsara kuma ta fito da ingantaccen kundin manufofi, wanda zai ja hankalin al’umma, wanda kuma da gaske ne cewa za a iya amfani da shi wajen kyautata wa talakawan Najeriya. Haka kuma, su tsaya da gaske su bar dimokradiyya ta yi aikinta a cikin jam’iyyar, ba kawai a rika dauki-dora ba.
Babu shakka dai an samu nasarar kafa kakkarfar jam’iyyar adawa a yanzu, ya rage ruwan jam’iyyar APC ta jajirce ta fuskanci aikinta da gaske, domin ta kasance mai kima da dacewa da kawo ingantaccen sauyi ga siyasar Najeriya.